MUHIMMIN SAKO GA MATA DA AKE TSANGWAMA 😓DAN BASUYI AURE BA.
Mashkur wali Nov 3, 07:53 AM

MUHIMMIN SAKO GA MATA DA AKE TSANGWAMA 😓DAN BASUYI AURE BA. 5

MUHIMMIN SAƘO GA MATA DA AKE TSANGWAMA😢 DAN BASUYI AURE BA. Abu na Farko Ƴar Uwa Ki Sani, Kuskure Na Farko ckn Gina Rayuwarki Shine Yin aure dan Kwayenki duk Sunyi, ko dan Kannenki sun Samoki✋😔, Mafi Girman Kuskure kuwa Shine Auran Wanda baki tabbatar da dacewarsa wjn zaman abokin Rayuwarki ba, Munin Kuskure Biyewa maganar mutane dake tsegumi Gameda rayuwarki(Alhalin ba Rayuwarsu bace!). Ya Ƴar uwa, kar kiji Tsoron Zamani dan shekarunki sunja bakiy aure ba, Karki manta cewa Galibi "Kyawun yanayi yafi zuwa ta ƙarshe ƙarshe😍" Ki Tuna Sayyida Khadijah(r.a) shekarunta sunka kai na manyanta amma karshe Ta Auri Annabi(s.a.w), kar kusantar shekaru su Riƙa baki tsoro✋, Ina miki Albishir duk Ya'yan Annabi(s.a.w) daga Khadijan suke, kuma annabi bayan ya aure ta bai sake aure ba sanda ta rasu😍 رضي الله عنها وأرضاها Dan haka kar kiji Tsoron zamani✋ , Allah ne mai Ƙaddara komai kuma Zamani a Hannunsa yake mai rahma(Subhanahu wa Ta'ala) Sau da yawa, Jinkiri Ckn al'amura kara musu kyau yake, Wa ya sanar dake, ƙila ma Allah(s.w.a) na miki wani Kyakkyawan tanadi ne Ckn Rayuwarki🤗 A ƙarshe, Bayan Karfafa miki gwiwa✊, Ina so Ki Nutsu ki tara hankalinki, Ƴar uwa, Aure Shine gini mafi daraja a rayuwarki, Karkiy gaggawa Ckn gina rayuwarki da maganar wasu(masu tsegumi) ko su waye✋😔 رضا الناس غاية لا تدرك "Yardar mutane duka buri ne da ba'a cin masa(har abada" So... Kar tsegumi ko surutun Mutane ya Dameki, Tunda Allah ya halicci duniya mutane magana suke ba kuma ranar da zasuy shiru. Ina miki Fatan Alheri, mu Haɗu a Nasiha ta gaba Insha Allah. ✍🏼Daga Ɗan uwa, kuma Ƙaninki Abdullahi Madachi(SheikhulHub)
post

Replies

(3)
Fatima Alfa Nov 3, 10:06 PM
♥️♥️♥️
reply 1
Habeebarty Nov 3, 10:52 PM
muna godiya ♥️ Allah ya saka da alkhairi
reply 1
Anonymous #1 Nov 4, 08:34 PM
wanna haka yake
reply 1

Related Posts


Trending

help a sister Relationship
what i'm going through due to lack of any relationship Relationship
i am thinking of Suicide General
Leaving someone that you love Relationship
Relationship Marriage
i found out my fiance has another relationship just before marriage Relationship
Introduction Lifestyle
Why the whole attitude ladies and their wahala Relationship
Nigeria My country😁😀😁😂😂 Entertainment
From strangers to Friends! ever met someone from this App? General
lets gist Entertainment
ana samun matar talaka anan kuwa? Relationship
Night chatter General
Successful Match Relationship