I am at a stage in my life that I'm thinking of doing something that will end up ruin my life ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญnice first daughter mama na ina da siblings mama da baba sun rabu tin ina primary 1 mun sha wahala sosai a gurin kishiyan mama na bata son mu ko kadan,ni da nake baba she hates me sosai...kullun cikin min sharri take gurin babana saboda ya tsane nii,haka naci gaba da rayuwa cikin kunciii da wahala ba mama sannan kuma babana kullun cikin hantara da kyaratayake ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญhaka abu yayi ta tafiya har na gama primary nayii shekara daya a gida banje secondary school bah baba yaki kainii,har sai wata rana uncle dina kanin babah yazo gida da safe ya ganni ya ce bana zuwa Makaranta ne nace mishii eh sanan yace akainii wata makaranta da aka bude kusa da sabuwa nan stepbrother na yake zuwa....da safe shiru shiru ba wanda yace in shirya haka na shirya na bi brother Schoolllll din naje office din head mistress na ce ance tamin interview shine ta kira uncle dina bayan na gama komai a saka ni a jss 1 na fara karatu a ranan ...haka problems sukai ta faruwa har baba na ya korenii daga gidan sa saboda kishiyan mamana ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญhaka na tafi gidan su mamana da dare...gashii su ba karfi ne dasu bah haka naci gaba da zama ina zuwa makaranta na samu na gama secondary school da kyar,mamana ta sake sabon aure yanzu ni gidan ganny na and I'm on my on..ni nake ma kaina komai mamana bata da karfii da zatamin wanii abu Babaaaa na manta rabon da yamin wani abu ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญrayuwa tamin zafiii Duk wanda zai taimaka maka sai ya nemi wani abu daga gurin ka ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญba cigaba da karatu gashii haryanzu banyii aure bah shima ansani a gaba..zuciyata tana rayamin in yarda da kawai in biye mazan tinda zasumin ban kudii in kula da kaina da siblings dina....ku tayani da addu'a Allah ya banii ikon cin jarabawa ๐๐๐๐๐๐
kar kiyi kinji sbd Allah yake jaraba ki yaga y imanin ki yake. Kuma mah wanda y sha wuya ynxu gaba ddi zai sha sbd mutane d yawa idn suka sha wuya gaba ddi suke sha๐ ki dage d addua d sallar dare kuma ki cire mah kanki wannan abun in sha Allah komai mai wuce wa ne๐
ki cigaba da Jin tsoron Allah ki kuma sa aranki cewa wannan jarabawa CE kuma in dai kin yi hakuri sauki na nan zuwa Insha Allah.Allah zai kawo Miki Mafita , hakuri da juriya sune matakin Nasara Amma Shi kuma sabon Allah ba abin da yake haifarwa Banda danasani. Allah ya baki ikon CIN wannan jarabawa sannan kuma Allah ya kawo Miki. Mafita a dukkan lamuranki.
Alhamdulillahi tunda kin fahimci cewa jarabawar Allah ce. Muna fata Allah ya baki nasara ki ci jarabawar..
Idan kika biye ma abin da zuciyar ki ke raya miki, gaskiya zaki yi asarar da har abada zaki yi ta nadama. Duk tsawon lokacin nan kin jure kin yi haฦuri sai kuma ki zo ki ษata lamarin. Allah na tare da masu haฦuri. Abin da haฦuri bai haifar ba rashin haฦurin ma ba zai haifar ba.
Ki mayar da lamarin ki ga Ubangiji, shi ne kaษai zai baki mafita.
Wannan zancen naki haka yake.
Allah ya sa mu dace
Ameen ameen
Allah sarki.Allah yabaki ikon cin jarabawarnan,yakuma kawomaki qarshen wahalarnan.karki biyewa zuciyarki kinji sis?kindaure yakusa xuwa qarshe.insha Allah you will smile at the end.we feel your pain kuma xamu taya da addua
Ameen
Allah sarki kowa arayuwa da irin yadda Allah yake yimishi jarabawa kita adduโa in sha Allah Komai xe wuce , Kita adduโa
Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un! Allah ya fitar dake daga wannan yanayin da kike ciki, Allah ya kawo miki dauki cikin gaggawa Alfarmar Annabi MUHAMMAD SAW. Kiyi ta addua, bayan wuya se dadi in sha Allah
kawai kidage da addua Komi me wucewane in sha allah watarana zezama history
×
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment