Ya zanyi don Allah ina naimam shawararku yan uwa😭😭😭
Anonymous Dec 29, 09:52 AM

Ya zanyi don Allah ina naimam shawararku yan uwa😭😭😭 0

mun kasance mu basu halibane to nasamu wani aiki inayi natara kudina nayi shawarar na fara sayayyan Kayan kitchen kafin aurena saboda kar sai aure yazo aga babu abinda muka saya shine nanemi shawara gun mahaifiyata sai tace aa musaya waken soya mu aje nan gaba zai qara kudi sai musaida muyi sayayya nace mata to Mujaheed muka saya mukakai Ajiya sai gashi jiya Wanda mukaba Ajiyan ta kirani a Waya wai anyi mata sata nima anhada da nawa amma ba duka suka daukaba shine nace to zanzo na kwashe sauran kawai na sayar shine da naje dauka naga saura daya kawai shine take fadamin wai ai mamana tun wancan satin tazo ta dauki buhu daya ta sayar bansaniba kuma wllh banga abinda ta sayaba nayi mata magana bata kulaniba😭😭😭😭wllh yanxu haka zuciyata jinake kamar zai buga ga Wanda aka sace ga kuma Wanda ta sayar na rassa yadda zanyi wllh ko magana ma ni yanxu banason yimata zuciyata nacemin in tada tsiya tabiyani kawai ba zaku gane me nake jiba wllh😭😭😭😭😭
post

Replies

(16)
Anonymous #1 Dec 29, 10:11 AM
take heart dear, sorry I feel ur pain. amma pha kisani bakiyi asara ba saboda wnda aka sace xasu biyaki duk daren dadewa nd wnda mamanki ta dauka kuma dake da dukiyarki duk nata ne toh kinga ba wnda kikayi asara koh daya akwai xafii kam amma kiyi hakuri sister
reply 4
Dr A A Dec 29, 10:26 AM
Don allah kada ki tada tsiya 😂 wllh ko kin tayar idan tace ba zata biya ba komai ba zaayi ba har gaban Allah sabida ita ta isa ga naki ko gaba daya ta siyar sai dai kiyi hkr shawara :: kada ki sakawa kanki damuwa akan wannan abun komai yana da lokaci sannan kuma inshaallah idan lokaci yayi ba zaa taba rasa abunda zaayi maki larura ba kije ki sayar da dayan ki saka kudi a account enki ko ki fara sayan kayan kina ajiyewa a gida wata antynki hka amma ki daina fushi da mahaifiyar ki ku dawo yanda kuke abaya haka kuma kici gana da kyautata mata kamar yanda kika saba zata ci gaba da alfahari dake haka kuma tana maki addua kuma ki kara rika cemata ta maki addua allah ya sanya labarka a rayuwar ki takan iya yuwa jarabawa ce allah yake so ya maki ta wannan bangaren ki kokari kifi karfin zuyarki kada ki yarda tasa kiyi fushi da mahaifiyar ki har yasa taji ba dadi kije ki shirya da ita na rokeki don allah kuma ki sani banza ba zata iya saka magaifiyar ki ta sayar da kayan ki ba zai iya yuwa lalura ce ta sa haka wacca kuma bata da mafita bayan tayi haka sannann kila koke kikaji dalilin da yasa ta sayar kila zaki iya bata dama ta sayar
reply 4
Zahrau haladu Dec 29, 10:52 AM
Haba sis gaskiya bamu goyan bayan ki tada tsiya ta biya ki ae da kai da kaya duk mallakan wuya ne baki San dalilin da yasa tayi hakan ba maybe wanan ne last option din ta pls kar ki bari mahaifiyar ki tayi fushi Dake akan abun duniya don Allah kada ki bari shedan yayi nasara a kanki kiyi hakuri kuyi addu'a insha Allah Allah zai kawo miki mafita hanyoyin Allah basa qarewa Allah yasa mufi karfin zuciyar mu Allah yayi ma iyayen mu Albarka ya saka masu da alkari
reply 1
Beelerh Dec 29, 11:06 AM
kiyi hakuri,Allah yasa haka shine mafi Alkhairi.
reply 1
Anonymous Dec 29, 11:10 AM
Seeyermerh Dec 29, 12:33 PM
kiyi hkr wanda mom naki ta dauka wnn ya tafi sbd mahaifiya ita ta kawo ku duniyar har kika samu amman su ki barsu da allah kiyi tawakalli Allah zai linka miki linkin balinkin kar ki bari zuciyarki tafi karfinki plz kifi karfinta 🙏
reply 0
Dr A A Dec 29, 02:23 PM

Ameen ya hayyu ya qayyum sister
reply 0
Yazeed Dec 29, 03:16 PM
haba sister idan rai yabaci kar hankali ya gushe ita din mahaifiyarki ce tanada iko akan dukiyar ki nasan akwai fushi amma Dan Allah kiyi hakuri
reply 0
Saudat abbas Dec 29, 06:59 PM
jarrabawace sis wlh kiyita addu'a Allah yasa Alkhairi ne 🙏kuma Allah yasa wanda suka dauke miki tsiyar suka dauka
reply 0
SallyMa Dec 30, 01:12 PM
Dan Allah sis Kar ki kara tada maganar nan gun mahaifiyarki. Allah ya kawo miki mafita.
reply 0
Sayyid hamzah Dec 30, 03:48 PM
karki fara wlh kin San uwa kuwa ai ko mai tayi ta cancanta tayi karki damu kanki ki bari kawai kici gaba da girmama ta Allah zai baki mafita
reply 0
Sayyid hamzah Dec 30, 03:49 PM
jama'a mu dinga Kula akan lamarin iyaye ba abin wasa bane Allah yasa mu dace
reply 0

Related Posts


Trending

friendship Relationship
Are you ready!!! General
Why is it that working class guys like me only meet idle ladies Relationship
Dear girls, Relationship
SEARCHING🥺🥺 General
Bare Ta Auri Dan Fulani General
What is your opinion on Jigida? General
Ya yanayin Sanyi a wajen ku at this time? General
Tambaya Entertainment
TEAM LEFE DOLE KO ASOKE LEFE Marriage
Guys on this app wan make me crazy Matchmaker
Boredom General
A Message to My Princess (unknown wife) Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure? Marriage