Ina fama da fistsarin kwance kuma an kusa Aure na,Ina neman shawara dan Allah da addua🥺😭🙏
Anonymous Apr 17, 11:04 PM

Ina fama da fistsarin kwance kuma an kusa Aure na,Ina neman shawara dan Allah da addua🥺😭🙏 0

Na kasance budurwa me shekaru 19 Allah ya jarabceni da lalurar nan ta fitsarin kwance shekara da shekaru lokachin da ina karamar yarinya banayi sai da na kai kusa 7years na fara ana cewa aljanu ne wasu na cewa lalura ce kaway anyi magani anyi magani amma har ynz ina yi ban daina ba musamman lokachin damuna da kuma yananyin sanyi da yanayin zafi ma ina yi amma ba sosai ba yanzu dai rabon da nayi nafi 2months gaskiya Abinda ke damuna shine bayan sallan nan za a kawo kudin aurena ina ta sake sake a raina shin na fada masa halin da nake ciki ko na kyaleshi saboda ina jin tsoro kar nayi aure dole zai gane dazu da yamma yace min zaizo ina ta tunani in fada masa ko kuwa na fara neman shawara ta wannan hanyar ban tsaida matsaya ba dai har yazo muna hira nake ce masa naga wani labari dazu a social media wani an hadashi aure da wata ashe tana fitsarin kwance bai sani ba basu fada masa ba sai daga baya bayan auren ya gane a lokachin dama baya sonta kuma sai ya kara tsanarta amma a hankali a hankali ya fara sonta daga karshe ma shi ya nema mata magani har ta warke sai nake ce masa a zamanin nan dai da wuya a samu maza irinsa sai nace masa shi idan shine zai iya zama da mace a haka? sai yace ya danganta idan akway tabbacin xata warke zai xauna da ita amma idan babu zai zauna da ita amma fah zai kara aure🥺 then I felt broke💔Amma nasan yana sona sosai wlh ina da wannan tabbacin kawai a lokachin Na rasa me zance masa gabadaya tunda ya tafi nake ta tunani shin in fada masa gaskiya ina da lalurar ko kuwa nayi shiru na kyaleshi??? dan Allah ku bani shawara kuma ina neman adduanku dan Allah😭🙏
post

Replies

(30)
Maryam Muhammad33 Apr 18, 01:14 AM
Allah sarki akwai Allah, just keep on praying sister kuma kicigaba da magani kinji, Allah yabaki lfy Ameen.😢🙏🏿
reply 4
Sgabdo Apr 18, 01:42 AM
Allah Sarki Allah Ya Baki Lafiya. Ya Rabaki da qanan Laruran
reply 1
Sgabdo Apr 18, 01:42 AM
Gaskia Dai Ki Fada Masa..Zaifi.
reply 3
Nasssss9 Apr 18, 04:16 AM
Allah sarki, Allah ya yaye miki, koda zaki fada mai ki fada masa a cikin lokacin da yake cikin farin ciki, kuma ba a waya ba, face to face zaifi, ki rage shan ruwa kafin ki kwanta, koda zakisha kisha kadan, kuma ki dinga sa alarm din @tleast every 5 hours bayan kin kwanta ki tashi, a haka zaki daina insha Allah, dama sai ansha Ruwa ake fitsari ai koh. Allah ya rufa mana asiri baki daya
reply 3
Anonymous #3 Apr 18, 05:03 AM
wayyo Allah ya baki lpy ammah kin kwada fatan rakumi edan ya bushe sai ki rika jikawa kina sha Allah yayaye maki fatan Ko yaya
reply 2
Anonymous #1 Apr 18, 07:44 AM
Wannan gaskiya babban larura ne wacce tafi karfin a boye ta saboda ko bayan auren zai fahimta. Ana yawan tambayan me yasa mutane ke chanza wa bayan aure! daya daga chikin dalilin kuwa rashin fadan gaskiya ne kafin aure da samun fahimta a tsakani. Daga bashi labarin irin hakan kinga yace ai aure zai kara kuma gaskiya magana komai kan iya faruwa fiye da hakan ma. kingani kar azo sai bayan kunyi aure ya fahimci kina da wannan larurar yaxo yana chi miki mutunci, ya dai na kyautata miki, ko ya sake ki ma, da dai sauran abubuwa marar dadi irin wanda kike jin labarin ko gani su ke faruwa da mata a gidajen su na aure. So shawarata anan ki fada masa gaskiyar maganan kawai ba sai ankai ga ya saka ki chikin tsangwama ba, idan zai iya yana so ki a hakan shikenan. idan kuma bazai iya ba yaje Allah zai kawo miki wadda zai soki a yadda kike. Kuma muna miki fatan Allah ya yaye miki ma. ya baki ikon chin wannan jarrabawar.
reply 5
Sadeeqsak Apr 18, 08:09 AM
Da farko dai, in kika bayyana aibi kikai gaskiya to sai Allah ya sanya maku Albarka a zamanku, in kuwa kikai sa6anin hakan to Allah zai kwashe maku albarka duka. Amma gaskiya ki rage shan ruwa in zaki kwanta. Allahu ya baki lapiya
reply 2
Anonymous #2 Apr 18, 12:16 PM
akwai malam albahas ki kirashi ya hada miki magani insha Allah za adace
reply 0
Anonymous Apr 18, 01:36 PM
Marieyerhm Apr 18, 04:07 PM
Allah ya yaye maki
reply 0
Xynb ibrhm Apr 18, 11:17 PM
Allah ya baki lfy
reply 0
Anonymous #2 Apr 18, 11:33 PM

yanada branch Bauchi da jos zan tura miki number shi
reply 0
Anonymous #4 Apr 19, 01:33 PM
Yar Uwa ki rufawa kanki asiri ki fada masa gaskiya. In kuma baza ki iya fada masa ba kar ki barshi ya kawo kayan.
reply 2
Anonymous Apr 19, 02:01 PM
Sayyid hamzah Apr 19, 08:34 PM

eh zai iya tura miki ai
reply 0
Anonymous Apr 19, 08:36 PM

okay na gode drop the number
reply 0
Sayyid hamzah Apr 19, 08:38 PM

okay 08035932047 albahas
reply 0
Anonymous Apr 19, 08:39 PM

❤️
reply 0
Anonymous #5 Apr 20, 01:02 AM
Gsky harkar aure bbu abinda xakayi hidden if Kayi daga baya yayi ko tayi finding out d truth, shiknn xa’a fara kin yadda da juna 🥺 Allah yabaki lpy kuma yabaki wanda ze kula dake
reply 1
Faizu muhammad Kabir Apr 20, 09:52 AM
Gaskiya u should tell him as soon as possible so as to avoid later disappointment.in har Yana sonki to Neman kafita zakuyi tunda wuri. Allah ya yaye Miki.
reply 1
Nana007 Apr 24, 07:37 PM
visit a psychiatrist pls most mutane sun gwada sun yi dace
reply 1
Yusuf adamu Ahmed May 15, 12:06 PM

Ameeen 📿 📿 📿 🤲 🕋 🤲
reply 0
Yusuf adamu Ahmed May 15, 12:06 PM
Allah yayaye
reply 0
Evraheem May 16, 09:48 PM
hmmm
reply 0

Related Posts


Trending

how i feel about women General
Are you ready!!! General
Dear girls, Relationship
SEARCHING🥺🥺 General
Bare Ta Auri Dan Fulani General
What is your opinion on Jigida? General
Ya yanayin Sanyi a wajen ku at this time? General
Tambaya Entertainment
TEAM LEFE DOLE KO ASOKE LEFE Marriage
Why do men do this dan Allah? General
Guys on this app wan make me crazy Matchmaker
Your Birthday. Entertainment
Boredom General
A Message to My Princess (unknown wife) Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure? Marriage