Anonymous
Apr 10, 04:27 AM
Important Q&A (ALAMOMIN DAREN LAILATUL QADRI
6
ALAMOMIN DAREN LAILATUL QADRI
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Assalamu Alaikum malam Dan Allah meye alamomin lailatul qadar da falalarsa kuma Ya ake gane daren lailatul qadri?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Wa'alaikumus Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu
Allah ﷻ ya fifita wani dare a cikin watan Ramadan ya ba shi wata daraja da ɗaukaka ta musamman, kuma ya keɓance shi da wata falala ta musamman wadda bai bawa sauran darare ba, wannan kuma zaɓi ne da ganin dama ne daga gare shi maɗaukakin sarki, domin yana yin abin da ya ga dama a cikin halittarsa.
Allah ya ce, “Daren Lailatul Qadari ya fi wata dubu alheri” (Alqadri : 3).
Ma’ana aiki a cikin wannan dare ya fi aikin wata dubu ba a daren Lailatul Qadari ba.
Allah Mai Girma Da Buwaya ya ce, “Aminci ne a cikinta har zuwa ɓullowa alfijir”. (Alqadri : 5)
Ma’ana dukkan wannan dare alheri ne, babu wani sharri a cikinsa tun daga farkonsa har zuwa ɓullowa alfijir.
Dare Ne Mai albarka. Allah Ya ce, “Haqiqa mun saukar da shi a cikin dare mai albarka. Haqiqa mu masu gargadi ne”. (Addukhan : 3).
Abdullahi dan Abbas ya ce, “Yana nufin daren lailatul Qadri”.
A Cikinsa Ne Aka Saukar Da Alkur'ani. Allah Yace “Haqiqa Mun saukar da shi a cikin daren Lailatul Qadri” (Alqadri : 1).
A Cikinsa Ake Qaddara Dukkan Abubuwan Shekara, Allah ya ce, “A cikinsa ake rarrabe kowanne lamari abin hukuntawa”
(Addukhan : 4).
Allah ya ɓoye wannan dare don musulmi ya yi qoqari da himma a goman qarshe ta Ramadan, musamman ma a dararen da suke mara, waɗanda su ne daren 21, 23, 25, 27, 29, saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ku kintaci daren Lailatul Qadri a cikin marar goman qarshe ta Ramadan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Wasu malamai sun yi bayanin cewa daren Lailatul Qadri yana yawo a tsakanin waɗannan darare (Wata shekarar wannan, wata shekarar wancan) saboda a yi aiki da dalilan da suka zo a kan haka baki ɗaya.
1 – Dare Ne Mai Haske, Babu Zafi Ko Sanyi A Cikinsa. An karbo daga Jabir ɗan Abdullahi – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Haqiqa ni an nuna min daren Lailatul Qadri, sannan an mantar da ni shi, yana goman qarshe na Ramadan, dare ne babu sanyi ko zafi a cikinsa, kuma mai haske ne, ba zafi ba sanyi (mai cutarwa acikinsa)” [Ibn Khuzaima ne ya rawaito shi].
2 – Rana Tana Fitowa Da Safiyar Daren Fara Tas Ba Haske Tare Da Ita. Yayin da aka tambayi Ubayyu dan Ka’abu – Allah ya yarda da shi – a kan alamomin daren Lailatul Qadri, sai ya ce, “Alamar da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ba mu labari ita ce, rana tana ɓullowa a wannan rana babu haske tare da ita” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya yi tsayuwa daren Lailatul Qadri yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
An karbo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, na ce, ya Rasulallahi, idan na dace da daren Lailatul Qadri, me zan yi addu’a da shi? Sai ya ce, ki ce;
اللّٰهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّيْ
“Allahumma Innaka Afuwwun Tuhibbul Afwa Fa’afu Anni*”
Ma’ana “Ya Allah kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka yi min afuwa” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
Allah ne mafi sani.