please ya ake ibadar nisfu sha'aban? urgent please
Anonymous Feb 24, 09:53 PM

please ya ake ibadar nisfu sha'aban? urgent please 1

aslm please yan uwana musulmai ina neman karin bayani ne game da daren yau (15 sha'aban) na nisfu sha'aban, falalar shi da kuma yanda ake ibadar shi it's urgent please nasan baxa a rasa malamai ba a cikin platform dinnan. a taimaka ayi mana cikakken bayani 🙏🙏
post

Replies

(2)
Anonymous #1 Feb 25, 11:10 AM
FALALAR NISFI SHA'ABAN Kamar yadda aka nemi a yi bayani ko da a takaice ne game da Nisfu Sha'aban. Annabi (sallahu alaihi wasallama) yakan azumce watan Sha'aban gabadaya, kamar yadda Al-Imamul Bukhari ya rawaito, Hadisi na: 1969, da Al-Imamu Muslim, Hadisi na:1156. Kuma Annabi (saw) ya kwadaitar da azumin ranaikun: 14,15,16, daga cikin Sha'aban. Har ma wanda wani uzuri ya hana shi Azumin wata rana a watan Sha'aban to sai ya rama Azumi 2 a maimakon dayan da ya sha a Sha'aaban. Bukhari:1983, Muslim:1161. Wadannan ingantattun Hadisai guda biyu sun nuna Falalar azumtar Sha'aban a dunkule ranar 15( Nisfu Sha'an) da sauran ranaikun watan. Annabi saw ya ce: idan 15 ga Watan Sha'aban ta zo, to ku raya daren da ibada, kuma ku azumci wunin; saboda Allah yana saukowa-iri wacce ta dace da matsayinsa- saman duniya yana cewa: ina mai neman gafara in gafarta masa? Ina mai neman arziki in arzuta shi? Ina wanda yake cikin bala'I in yaye masa? Ina wanda yake neman kaza da kaza in yi masa? Ina...? Ina,,.?haka har alfijir ya hudo. Ibn Majah ya ruwaito. Akwai Hadisai da dama a kan Falalar raya Dare da wunin nisfu Sha'aban bayan wannan kamar wadanda Tirmizi da Ahmad da Ibn Majah da wasu suka ruwaito, wasu suna da rauni, amma ya halatta a yi aiki da su a irin wannan mahalli, kai al-Imamun Nawawi ma cewa ya yi mustahabbi ne yin aiki da su. A dunqule dai hadisan suna nufin: -Lallai Annabi saw yana jajircewa a Daren Nisfi Sha'aban wajen bauta wa Allah (T) -Allah SWT yana tajajji ga bayinsa yana cewa da su: ko fuskanto gare ni! kowa ya nemi abin da yake so, qofofin kyautoci a bude suke hanhai!! -ya kamata a dage da yin ibada tun daga farkonsa har karshe, kuma a azumci ranar, don ita ma falalarta kamar ta daren ce. -yawaita neman gafara saboda Allah TWT yana gafarta wa dukkanin halittarsa, in banda wanda ba ya biyayya ga iyayensa, da azzalumi da fajiri da dai duk wanda yake aikata abin da yake jawo fishin Allah in bai tuba ba. -wannan ita ce HUDBAR da mallai da yawa sukayi a Juma'ar da ta wuce: (10/Shaban 1445129/6/12kenan( wallahu a'lam) "شعبان ١٤٤٥ هجرة" Daren Nisfu Shaaban zai kama Asabar(السبت) 14 ga watan Shaaban(شعبان) 14/8/1445 hijjrah dai dai da 24/2/2024. (Allah shi ne Masani.) 3/7/2018(c)
reply 1

Related Posts


Trending

Wane course ne idan mutum yayi ze samu aiki General
Buhari retire Politics
Family palava General
what's bad in delaying marriage? Marriage
Is it okay to send nudes to your boyfriend? Advice
Addiction problem Advice
I need an advice about our relationship with my cousin Relationship
Miji na baya saduwa da ni? should i do this? Marriage
unjust love Advice
Should i do it? she's tempting me Advice
Friend request Advice
Warning to others! How porn destroyed my life Advice
I need Advice Advice
i want to get married ???? Marriage
Female best friend General
Looking for poetic lady Meetup
advice pls Relationship