As-salamu alaika wa rahmatullah wa baraka tuhu
Yaya ake zakkan fidda kai, kuma a yaushe akeyi, Nagode.
*ZAKKAR FIDDA-KAI*
********************
Zakkar fidda-kai itace zakkar da ake kira Zakkar buÉ—a-baki, domin a banbanta ta da Zakkar dukiya.
*HUKUNCIN TA:*
••••••••••••••••••••
Zakkar fidda-kai, wajibi ce a kan kowane Musulmi, namiji da mace, yaro da babba, É—a ne ko bawa.
*ME AKE BAYARWA:*
•••••••••••••••••••••••••
Ana bayar da kwano guda, wato muddun Nabi huÉ—u, a kowane mutum, daga abincin da mutanen gari sukafi amfani dashi.
Idan ya zama shinkafa akafi ci a yankin unguwarku, to ita zaka É—auka kayi da ita, kada ka bada gero, ko dawa ko masara.
Amma idan mutanen unguwar sunfi cin marasa, shine mafi rinjayen abincinsu saika basu masara, kamar yadda larabawa suke bada dabino domin shine mafificin abincin su.
Sannan kuma wajibi ne ka bayar da shinkafa mai kyau, kada ka bayar da abinda kai bazaka iya cinsa ba.
Sannan mai gida ne yake fitarwa da iyalinsa waÉ—anda yake ciyarwa, bayan ya fitar wa kansa.
*YAUSHE AKE FITAR DA ITA:*
••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Ana fitar da ita a rabar a safiyar sallah, kafin a tafi sallar Idi, idan kuwa aka bari har sai bayan sallar Idi, to ba zakka sunan ta ba, ta koma daidai da kowace sadaka.
Amma kuma ya halatta a bayar da ita tun kwana É—aya ko biyu kafin Idi.
Domin hakan wasu Sahabban Annabi
{s.a.w} suke yi.
*SUWA AKE BAWA:*
••••••••••••••••••••••••
Ana bayar da ita ne ga fakirai da miskinai, amma fa wannan baya nufin idan kai fakiri ne ko miskini shikenan ba zaka fitar ba.
Dole ne ka bayar ga wanda yafika talauci, domin bata sauka daga kan mutum sai idan ya zama a safiyar Idi ba shida abinda zai fitar bayan ya ciyar da iyalinsa.
Mutuƙar kanada abinci a gidanka, to wajibi me ka fitar, ko kuma idan ankawo maka kaima saika fitarwa kanka daga cikin abinda aka kawo maka, mutuƙar zaka sami ragowar abinci da zsi rage kuci a gida.
*INA AKE KAIWA:*
•••••••••••••••••••••
Idan akwai wurin da hukuma ta ware, to yana da kyau akai can, amma lallai akai a ƙalla kwana biyu kafin ranar Sallar, domin hukuma ta raba da wuri.
Idan kuwa babu, to sai mutum ya rabawa fakiran da kansa.
Babu laifi a bawa limami ko malamin unguwa idan fakiri ne.
*KO ZA'A IYA BADA WANI ABU A MAIMAKONTA*
Dole ne a bayar da abinci, sai idan babu abincin ko ba zai yi amfani ba,
Kamar wasu ƙasasen da basa karɓar sadakar abinci, to saika kimanta da kuɗi ko wani abu da suke iya karɓa.
*HIKIMARTA:*
••••••••••••••••
Babbar hikimarta, itace ciyar da miskinai, da kuma cike kura-kuran da mai azumi yayi da ladanta.
Idan mutum ya fitar da za'a cike masa inda ya sami rauni acikin Azuminsa, irinsu gulma, zagi, kallon batsa, da wasu laifuka wanda basa karya Azumi, amma suna raunana ladan Azumi, to sai a cike masa waÉ—annan gurare.
ALLAH shine mafi sani.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.
ALLAH ka yafe mana zunubanmu baki É—ayanmu Ameen.
Jazakallahu Khairan
×
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment