Shin yaushe ne lokacin buda baki? (amsa)
Anonymous Apr 4, 02:39 PM

Shin yaushe ne lokacin buda baki? (amsa) 4

LOKACIN SHAN RUWA (BUƊA BAKI) : 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓ : Assalamu Alaikum malam khamis Muna godiya sosai. Allah ya saka muku da alkhairi Ameen. Tambaya ta anan shine Yaushe ne lokacin buɗa baki (shan ruwa)? : 𝐀𝐌𝐒𝐀❗️ : Lokacin buɗa baki ya na tabbata ne da zarar rana ta faɗi. Dalili kuwa shine, hadisin da aka karbo daga Sahk ibn sa'ad, ya tabbata acikin Sahīhul Bukhārī daga Sahl Ibn Sa’ad yace: haqiqa Manzon Allah yace: Mutane ba zasu gushe tare da alheri ba matuqar suna gaggauta buɗa baki. Amma abin mamaki ayanzu sai kaga waɗansu mutane suna jinkirta buɗa baki har sai sunyi sallar magriba. Haqiqa yin haka ba qaramin kuskure bane, domin ya saɓawa koyarwar Manzon Allah ﷺ. Waɗansuma sai kaji su na cewa sai taurari sun bayyana, sannan suyi buɗa baki. Irin waɗannan mutane a tunanin su yin haka shine daidai, alhali kuwa ya saɓawa Sunnah, kamar yadda akayi bayani a hadisin daya gabata. Manzon Allahﷺ Yana cewa: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم ﺑﻜﺮﻭﺍ ﺑﺎﻹﻓﻄﺎﺭ ﻭ ﺃﺧﺮﻭﺍ ﺍﻟﺴﺤﻮﺭ ‏ [📕ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ.(2835)] Manzon Allah (saw) Yãce: Ku Gaggauta Shan-ruwa, Kuma ku Jinkirta Sahur. قال رسول الله صلى الله عليه وسلم ﺛﻼﺙ ﻣﻦ ﺃﺧﻼﻕ ﺍﻟﻨﺒﻮﺓ: ﺗﻌﺠﻴﻞ ﺍﻹﻓﻄﺎﺭ، ﻭﺗﺄﺧﻴﺮﺍﻟﺴﺤﻮﺭ، ﻭﻭﺿﻊ ﺍﻟﻴﻤﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺸﻤﺎﻝ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ [📗ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ.(3038)] Manzon Allah (saw) Yãce: Abubuwa Uku Suna daga Cikin ɗabi'un Annabta, 1- Gaggauta Shan-ruwa, 2- Jinkirta Sahur, 3- 'Dora hannun dãma akan hagu a Sallah. Haka hadisin da aka karbo daga Abdullahi Ibn Abī Auf yace: "ya kasance tare da Manzon Allah ﷺ a lokacin tafiya suna azumi, sai rana ta faɗi, sai Manzon Allah ﷺ yace da wani daga cikin sahabbansa ya sauka ya shirya musu kayan buɗa baki sai, sahabin yace: "Ya Manzon Allah da sauran rana, akayi haka har sau uku, Manzon Allah ﷺ na cewa dashi ya shirya musu abin buɗa baki. Daga karshe bayan sun kammala sai Annabi yace: “Idan kuka ga dare ya gabato daga nan (wato rana ta faɗi), haqiqa mai azumi ya buɗe bakinsa (ana nufin koya sha ruwa ko bai sha ba) Bukhari da Muslim suka ruwaito shi. Daga Ansa bn Malik(RA) ya ce: Manzon Allah(ﷺ) ya kasance yana yin buɗe baki kafin ya yi sallah da danyen dabino, idan bai samu danyen dabino ba sai yayi da busassun dabino, idan kuma bai samu busasshen ba, sai ya kurɓi wasu kurɓi na ruwa". Tirmidhi ya ruwaitoshi ALLAH NE MAFI SANI
post

Replies

(0)

Related Posts


Trending

friendship Relationship
Are you ready!!! General
Why is it that working class guys like me only meet idle ladies Relationship
Dear girls, Relationship
SEARCHING🥺🥺 General
Bare Ta Auri Dan Fulani General
What is your opinion on Jigida? General
Tambaya Entertainment
TEAM LEFE DOLE KO ASOKE LEFE Marriage
Why do men do this dan Allah? General
Guys on this app wan make me crazy Matchmaker
Your Birthday. Entertainment
Boredom General
A Message to My Princess (unknown wife) Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure? Marriage