Nizam
Aug 20, 03:46 PM
Gargadi Ga Alumar Hausawa
0
Wata sabuwar alada ce da ta shigo local hausa community da na lura, kuma naga yakamata a gargadi alumma.
Watau iyaye na yin kuskure, wajen banbanta ga tarbiyar yara.
Yarinya mace har tai aure sai ka ga itace islamiyya, itace, harda itace, boko, talla itace, in aike ya tashi a gida itace, ko kasuwa ne itace. ai ta rike ta gamgam ana dora ta kan hanya wai a karamin tunaninmu muna so ta kyautatta don ta samu miji nagari, kuma eh yarinya indai ba talla ake dora mata aba kokuma barinta ake zuwa yawo gidajen biki ba, eh sau dayawa ana saa… sai kaga yarinya ta tashi kamila da hankali kuma inshaa allahu in kai saa mai tsoron allah sai kaga alamarin abun shaawa. Duk wannan dai dai ne.
Inda kuskuren yake shine wajen tarbiyan maza, santari wai sai kaga wai in yaro ya wuce jss 3 sai kaga iyaye sun fara sakan mai alamuransa. In ma yace bazai je boko sai a yardan mai. Balle kuma islamiyya baa Magana. Yanzu un kaje any islamiyya anan arewa alkawari sai kaga 80% duk matane, maza baa masu dole suje. Yo yaro bama ya yini gidansu baa san ina yake ba ina zaa kawo shi islamiyya, shidai amfanin shi lokacin damuna ya taya uban a gona. Daga nan ba ruwansa da mike faruwa gida. In ka tambaye shi ko iyayen sun tambaye shi sai yace ya fita dako kuma duk karya ce, kokuma kaji ance yana farauta kokuma kaji ance yana gidan dambe ko gidan gala ko gidan solo. Kokuma duk wani abu marar amfani. Shi da gida in yaji yunwa yazo gida yasha fate, ya ci tuwo. Kai abun kunya in ma yaro baya son fita yakai wani shekaru sai kaga wai koranshi akeyi ana cewa zam gida na mata ne yaje yai harka da abokansa. Duk iyaye na manta in yaro ya fita ko da kanshi kokuma in an korashi to fa zai fada chikin yan daba ne kokuma chikin yan shaye shaye, kokuma shikin yan fashi kokuma chikin yan kwace kan titi, abun dai baa kirgawa. Yaro bakasan harkokinshi, kila ma kana kwana da dan fashi, ko wani babban dan chacha ko dan daudu cikin gida bakasani. Gidajen hausawa ma da ake dakunan maza a waje baa san yaushe ya shigo ba ko ya fita koma in yak wan gida ba shin suma mazan ba yayanmu bane, namaji kadage kayi tarbiyar shi ma ya ka kare balle ka sake shi duniya.
Abun da muka mantawa yarin yar nan da muke ta killace wa muna so ta samo miji na gari kashi 7 chikin 10 irin wannan yaron da ka sakar wa duniya fa irin shi fa zata jajibo tace tayi saurayi, ai masu aure. Shiya sa yanzu sai kaga yarinya masha allahu kana ta daukin wa zata kawo amma daga takawo mijin sai ka ganshi wani gaja, ko wani santolo , gashi gashi dai, bai chika mutumba ko a furucin shi. Kuma ba yanda zakai dole ka aura mata haka. Domin bakada wani wanda ya fishi da zaka kawo mata itama ta duba ta duba bata da wani wanda ya fishi…
Yakamata alumma ta duba. Kada mu manta mu muka haifi yaran mu basu suka haifemu ba. Yanzu mutum in yaro ya gagare shi yace yabar mai gida sai kaji kowa yayi ca kanshi, yana chewa yai hakuri amma yaro sai ya zauna don ai gidan ubansa ne. kamar yanada wani permernent seat a gidan.
Malamai a fadakar don Allah. Na gode