SHAWARA ga wanda mahaifiyar sa ke raye π
1 Kayi amfani da damar ka na tana raye ka bata duk wata kulawa da take buqata daidai ikon ka
2 Kayi kokari wajan kaucewa duk wani abu da kaga bata so,koda zuciyar ka tana so,kaucewa abinda take so,zai jawo maka matsala ta inda bakai zato ba
3 Kowace dama a rayuwa idan ta kubuce ana iya dawo da ita,amma mahaifiya guda daya ce,idan ta tafi ba zata dawo baπ
4 Aljannar ka,farin cikin ka,nasarar ka a rayuwa,tana da alaqa ne da irin kulawar daka bawa mahaifi da mahaifiyar ka,dan haka dan uwa ka kula sosai.
Baka gane hakikanin maanar rayuwa,sai lokacin daka duba dakin mahaifiyar ka kaga cewa bata nan,kace Baaba na tafi kasuwa kaji bata amsa ba,ka kawo mata abinda take so baka ji ta sanya maka albarka ba,anan ne zaka gane hakikar maanar rayuwa,anan zaka ga zahirin yan uwan ta masu zuwa tana raye,anan ne zaka gane rayuwar mahaifiyar ka a duniya komai tsufan ta a duniya,rahma ce gare ka matukaπ
Allah dan tsantsar rahmar ka da karamcin ka,ka jaddada rahma ga dukkan wanda mahaifiyar sa ta rasu,ka kara mana juriya da hakuri a wannan rayuwa
ni dai ta rasu 13 yrs ago
Allah yyi mata rahama
Ameen
Ameen Ya Rabbil Alamin
Ameen
Ni 8 years
Allah shi bamu wanda zasu samu farin ciki
Γmeen ya Rahman π sister
Ameen y Allah
gaskiya ne, ka Ζara fadakar da mu, mu tashi tsaye, mamana tana nan a raye kuma ina iya bakin kokarina amma wannan maganar ta sa zan kara zage dantse wajen kyautata mata.
ina fatan Allah ya jiΖan iyayenmu, waΙanda na su ke raye kamarmu, Allah ya bamu ikon kyautata musu
Amin a dage sosai dan uwaβ
Amin, AllΓ h yaji kanta da rahama
Amin Allah yaji kanta da rahama,sai adage da mata addu'a,da yawan yin sadaka Allah ya kai ladan gareta,na tabbta zataji ddi sosai
Nagode sosai
Tarasu 13yrx knn I wish tana raye taga girmana πππ«, Allah yajikan dukkan musulmai Ameen
Allah yaimata gafaraππ€§ Same nima 13yrx knn
Allah sarki π₯² gwanda mu Maza
Allah sarki, Allah yaji kanta amin
Allah y gafarta Mata,kema ki dage da mata addu'a,kiyi la'ilaha ilallah dayawa kice Allah yakai ladan kabarinta,snn ki rik yawaita mata sadaka ladan gareta,inda dama ki shuka bishiya ladan gareta kinji,zatayi alfahari dake rnr lahira inshallah
Ameen ya rabbil izzati π€²π»π«
Nagode Sosai
Allah yabaka mece tagari if Kayi aure Allah yabaku xmn Lpy π
Amin amin thanks, banyi bah dai tukun π
Allah ya jikanta yasa aljannace makomarta
Allah ya jikanta yasa aljannace makomarta
Ameeen sis tnxβ€οΈ
Allah yabada sa'a muma munkusa π
Allah ya jikanta yasa tana jannatul firdausi π
Amin
×
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment