Anonymous
Apr 12, 10:36 PM
importan Q&A (HUKUNCIN AMFANI DA MAGANIN INHELA GA MAI AZUMI
1
HUKUNCIN AMFANI DA MAGANIN INHELA GA MAI AZUMI
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Menene hukuncin amfani da maganin fesa iska a cikin bakin mai azumi da rana (wato, inhela), saboda ciwon quncin qirji ko wahalar numfashi (Asma)?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Hukuncinsa shi ne halacci; idan har lalura ta buqatar da mutum zuwa ga hakan, saboda fadin Allah Mabuwayi da daukaka a cikin "suratul An'aam ayata 119":
وَقَدْ فَصَّلَ لَكُم مَّا حَرَّمَ عَلَيْكُمْ إِلَّا مَا اضْطُرِرْتُمْ إِلَيْهِ
Ma'ana: "Kuma ya muku bayani na dalla-dallan abinda ya haramta akanku, sai dai wanda lalura ta buqatar da ku zuwa gare shi"
:
Kuma saboda kasancewar inhela baya kamantacceniya da ci ko sha, sai ya yi kama da jinin mutum da ake dauka don aunawa ko bincike, ko kamar allurar da ba a sanya abinci a cikinta ba.
:
Duba cikin littafin: TUHFATUL IKHWAN BI AJWIBATIN MUHIMMATI TATA'ALLAQU BI ARKAANIL ISLAAM.
:
MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 265).
Allah ta'ala yasa mudace.
: