ZABEN ABOKIN ZAMA
Alhaji Hamza Apr 12, 05:27 AM

ZABEN ABOKIN ZAMA 1

Ni dai nakan ce, matsalar da aketa magana akan zaben abokin zaman aure; muna bari jaki me, mu rika bugun taiki. Dalilina shine, iyaye a yanzu sun cire/ an cire hannunsu daga zabarwa yaransu (maza da mata) abokin zama, sai dai idan yaran sun gama sharholiyarsu sannan a nemi iyaye su daura aure sau da yawa. A ka'ida iyaye ne za su duba Wanda ya cancanta ga 'yarsu/dansu sai su zaba musu, domin wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi, ballantana Wanda shi ya haifeka, to sai aka ce mana wannan sunanshi auren dole, kuma duk muka yarda (Dan haka iyaye suka janye hannunsu, mu kuma 'ya'yan muke gaban kanmu). Sannan mun daina neman zabin Allah sai a Baki kawai, za'ayi aure an tafi wurin boka ko dan duba, ko kuma idan anyi Istikhara ta shari'a to amma akwai abinda mutum ya zabarwa kanshi already kawai yayi ta ne a matsayin zaiyiwa Allah wayo. Ko kaji muna 'ai baza mu iya hakurin da kakanninmu sukayi ba a zaman aure saboda mun waye' to tunda bazamu iya abinda sukayi ba; ai bazamu sa rai da samun sakamako irinnasu ba kuwa (ko a makaranta idan bazaka iya nacin da wancan yakeyi ba da juriya wajen karatu ai kasan sakamkonku bazai zama dai-dai ba. Allah Ya sa mu farka da wuri.
post

Replies

(2)
Anonymous #1 Apr 12, 01:05 PM
Ameen ya RABBIL Alamin jazakallah khairan
reply 1
Khadija Apr 15, 01:28 PM

Ameen ya hayyu ya kayyum
reply 1

Related Posts


Trending

Wane course ne idan mutum yayi ze samu aiki General
Buhari retire Politics
Family palava General
what's bad in delaying marriage? Marriage
how i feel about women General
Is it okay to send nudes to your boyfriend? Advice
I need an advice about our relationship with my cousin Relationship
Miji na baya saduwa da ni? should i do this? Marriage
unjust love Advice
Should i do it? she's tempting me Advice
Friend request Advice
Warning to others! How porn destroyed my life Advice
What do ladies mean by "Financial stability" in men?? General
I need Advice Advice
Looking for poetic lady Meetup
Seeking for friends General
a never ending love General