HUKUNCIN SADUWA DA IYALI HAR ZUWA WAYEWAR GARI A WATAN RAMADHAN
Abubakar Mahmoud May 24, 05:27 AM

HUKUNCIN SADUWA DA IYALI HAR ZUWA WAYEWAR GARI A WATAN RAMADHAN 4

YA AZUMINSU YA KE !? YA SADU DA IYALINSA A DAREN RAMADAN, HAR ALFIJIR YA KETO BAI SANI BA: ------------------------------------------------------------ AMSA: Lokacin da mutum yake saduwa da iyalinsa a daren Ramadan, ba tare da ya sani ba har alfijir ya bullo, ko kuma aka kira sallah, ko kuma suka ji an tayar da ikama, to sai mijin yai maza ya zare gabansa daga farjin matarsa. Shike nan azuminsu yana nan daram, kawai sai su yi wanka su ci gaba da azuminsu, matukar ba su ci gaba da saduwar ba bayan sun fahimci bullowar alfijir. Amma bayan sun ji an kira sallah, kuma sun tabbatar da hudowar alfijir amma sai suka ci gaba da saduwarsu, to azuminsu ya karye. Don haka bayan Ramadan duk su biyun za su rama azumin wannan yinin, sannan kuma su yi kaffara kamar haka: 1. Ko su 'yanta baiwa/bawa (sai dai yanzu babu bayi). 2. Ko su yi azumi 60, idan ba za su iya ba, saboda wani uzuri na shari'a, to... 3. Sai su ciyar da miskinai (mabukata) guda 60. 4. Idan tsananin talauci ya sa ba za su iya ciyar da mutum sittin ba, to kaffarar ta saraya a kansu. Wannan ita ce amsar da malamai suka bayar, kamar sheikh Bin Baaz da Sheikh Uthaimeen da sauransu. Wallahu a'alam. Gae neman karin bayani daga malamai, to ga abin da SHEIKH UTHAIMEEN R. Ya ce game da wannan mas'alar. ﻭﺳﺌﻞ ﺍﻟﺸﻴﺦ عثيمين ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ﺇﻧﺴﺎﻥ ﺣﺪﻳﺚ ﻋﻬﺪ ﺑﺎﻟﺰﻭﺍﺝ، ﻭﺃﺗﻰ ﺃﻫﻠﻪ ﻓﻲ ﺁﺧﺮ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻇﻨﺎً ﻣﻨﻪ ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺑﺎﻕ، ﻭﺇﺫﺍ ﺑﺎﻹﻗﺎﻣﺔ ﺗﻘﺎﻡ ﻓﻤﺎ ﺗﻘﻮﻟﻮﻥ؟ ﻫﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻲﺀ؟ ﻓﺄﺟﺎﺏ : " ﻻ ، ﻣﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻲﺀ ، ﻻ ﺇﺛﻢ ، ﻭﻻ ﻛﻔﺎﺭﺓ ، ﻭﻻ ﻗﻀﺎﺀ ؛ ﻷﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻗﺎﻝ : ‏( ﻓَﺎﻵﻥَ ﺑَﺎﺷِﺮُﻭﻫُﻦَّ ‏) ﺃﻱ : ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ‏( ﻭَﻛُﻠُﻮﺍ ﻭَﺍﺷْﺮَﺑُﻮﺍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺘَﺒَﻴَّﻦَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺨَﻴْﻂُ ﺍﻷَﺑْﻴَﺾُ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺨَﻴْﻂِ ﺍﻷَﺳْﻮَﺩِ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻔَﺠْﺮِ ‏) ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ .187/ ﻓﺎﻟﺜﻼﺛﺔ ﻛﻠﻬﺎ ﺳﻮﺍﺀ : ﻣﺒﺎﺷﺮﺓ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻭﺍﻷﻛﻞ ﻭﺍﻟﺸﺮﺏ ، ﻭﻻ ﺩﻟﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻖ ﺑﻴﻨﻬﺎ، ﻛﻠﻬﺎ ﻣﻦ ﻣﺤﻈﻮﺭﺍﺕ ﺍﻟﺼﻴﺎﻡ، ﻭﺇﺫﺍ ﻭﻗﻌﺖ ﻋﻠﻰ ﻭﺟﻪ ﺍﻟﺠﻬﻞ ﺃﻭ ﺍﻟﻨﺴﻴﺎﻥ ﻓﻼ ﺷﻲﺀ " ﺍﻧﺘﻬﻰ ﻣﻦ " ﺍﻟﻠﻘﺎﺀ ﺍﻟﺸﻬﺮﻱ " Dalibinku: Bukhari Musa Adam 17/09/1440 = 22/5/19
post

Replies

(0)

Related Posts


Trending

how i feel about women General
Are you ready!!! General
Why is it that working class guys like me only meet idle ladies Relationship
Dear girls, Relationship
Bare Ta Auri Dan Fulani General
What is your opinion on Jigida? General
Ya yanayin Sanyi a wajen ku at this time? General
Tambaya Entertainment
TEAM LEFE DOLE KO ASOKE LEFE Marriage
Why do men do this dan Allah? General
Guys on this app wan make me crazy Matchmaker
Your Birthday. Entertainment
Boredom General
A Message to My Princess (unknown wife) Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure? Marriage