I am divorced my mom wants me to return but I DON'T. please ku taimaka mini da shawara
Anonymous Apr 22, 10:08 PM

I am divorced my mom wants me to return but I DON'T. please ku taimaka mini da shawara 1

na kasance yarinya karama da nayi aure a 18years kwata kwata aurena tun yana 2weeks na farà fiskanta matsala duk sanda zai ce na tafi gida in na koma gida sai yaje ya bada hakura a gida kuma ace nayi hakuri na koma haka ya faru Har sau 6 Har ya Kai wani lokacin ya sakeni amma sai ya musu daga baya ya fito ya fada cewa ya sake ni ya Kara nada hakuri a gida cewa shi bai san mai ya same shi ba yake haka aka mayar da ni sai gashi randa aka farà azumi lokacin shan ruwa haka kawai yace min ya sake ni ya bani takarda na koma gida a washe garin ya kara zuwa gidan mu ya bada hakuri yace ya mayar da ni toh yanzu un uwana sunce sun gaji da halinshin nan don kuntatamin yake yi nake hakuri sunce bazan koma ba in har bani nace Zan koma ba Nima kuma bana so na koma wallahi bana Jin son kara ganin sa balle zama da shi toh matsalan shine ita mahaifiyata tace nayi hakuri na kara komawa muta addua Allah shirye shi kowa yaki saboda kowa yasan yadda nasha wahala a gidan nima kuma bana son komawa don yanzu haka nayi 1month a gida ina nan ina lissafa idda na amma yadda mahaifiyata ta damu na koma yana damuna don Allah mai mafita note:makaryaci ne kuma yana changer magana kuma baya sallah baya zama da kowa lafiya ko cikin mutane baya zama baya kyautatawa en uwanshi Har mamanshi bata fadan magana mai kyau a kanshi
post

Replies

(11)
Rukaiya Muhammad Apr 22, 10:30 PM
complicated issue ne wannan gaskiya sis.first dai mahaifiyarki tanuna kikoma to amma kintaba zaunar da ita kin nunamata halin dakike ciki?like zama na uwa da ya?because inhar you guys have mother and daughter talk deeply yakamata tamaki adalci gaskiya. 2ndly gaskiya involved waenda suka daura maki aure ma'ana walee dinki,they are very important in this inhar basu saniba and kitabbata kinfada masu komai. lastly talk to your mum about the risk involved pls.insha Allah xaadace.
reply 2
Muhammad najib Apr 22, 10:56 PM
na Yadda da dukkan abin da rukaiya ta fada kiyi Amfani da shawararta sai dai Dan kari da zanyi . shine be kamata ki koma BA duba da Yadda ki kace baya sallah, wannan kadai ya isa hujjar ma da Zata sa Kar ki koma gidan Shi domin ko da ma ace kuna zaune lfy Amma to AI Shi baya zaune lfy da mahaliccin Shi Don baya sallah gashi kuma ya siffanta da wasu daka cikin siffofin munafikai wato karya , Abu na gaba shine rashin muamalat da mutane. ki zauna da mahaifiyarki ,ki fada Mata duk wani Abu da ki kasani Kar ki boye komai , ki nunar Mata da rashin yin sallah kadai Yana sa a Raba aure koda ana zaune lfy sannan Wanda ya kasa ba Allah hakkinsa na bauta taya Ake tunanin zai iya rike aure. Allah ya kawo Miki mafita aduk lamuran ki sannan Allah ya Baku ikon bin tafarkin manzon tsira s.a.w, Allah ya baki ikon yima iyayen ki biyayya Akan abin da be sabawa Shari,a ba .
reply 2
Anonymous Apr 22, 11:01 PM

dukka tasan komai Har ita last case din akayi ta kirashi ta fada masa in dai haka halinshi yake bazai iya zama da kowa ba kuma waliyyansa ma tun a second case sukace baxasu kara shiga ba in ya kara don yana zubar musu da mutumci ita wai damuwa ta Kar ina yarinya aure na ya mutu ko shekara bai yi ba
reply 1
Anonymous Apr 22, 11:02 PM

ameen ameen ya Allah dukka tasan komai shiyasa abun yake daure min kai ko ita Zata fada duk abunda na fada a kanshi amma wai in yi hakuri
reply 0
Muhammad najib Apr 23, 08:02 AM

eh hakan zai iya faruwa sbd yawancin iyaye Mata basa son suga yayansu sun Zama zawarawa musamman in suna da karancin shekaru ko kuma a CE auran BA wani dadewa ya yiba, ki cigaba da addu,a Allah zai kawo mafita Insha Allah
reply 2
Sadeeqsak Apr 23, 09:40 AM
ki amsa maganar mahaifiyar taki ki ta masa Addu’a, akwai alkhairi mai yawa cikin biyayyar iyaye. Sannan ki riki mahaifiyarsa ta na masa Addu’a zai iya yiwuwa muggan kalamantavne suka zautar dashi. Tabbas yana son ki. Amma dai ki cigaba da mai Addu’a, ki koma in har sakin bai kai 3 ba.
reply 1
Anonymous #1 Apr 23, 01:42 PM
hmmm toh A musulunce tunda yace ya maidaki kin maidu... so kawai hakuri zakiyi ya sake ki saki ukku...Amma in har kikaje kikayi Wani auren toh kin yi aure kan Aure.... duk yayan da zaki Haifa sun zama shegu
reply 1
Anonymous #2 Apr 23, 10:16 PM
Idai baku aihu ba toh karki koma abinki. Halinsa ba mai kyau bane gaskiya
reply 1
Bulama A Apr 25, 06:36 PM
Ki bawa mahaifiyar ki haukuri, ke kuma Allah ya kawo wani miji nagari
reply 0
Mustapha Sani Abdullahi Apr 27, 10:54 AM
Shawara ta farko tunda baya Sallah kuma mahaifiyar shi bata jindadin shi don haka ki zauna da mahaifiyar ki fahimtar da ita illar zama dashi. domin nan gaba idan kika fara haihuwa Zai wulakanta ki dake da ya'yan ki sannan kuma dole ita mahaifiyar Taki zata rike ku idan ya Koro ku.
reply 0
Rukaiya Muhammad May 28, 01:47 PM

hmmmm ikon Allah. kiyiwa mahaifiyarki biyayya kuma kidage da adduar dakuma istigifari tayu kema akwai abun dakikayiwa Allah ya jarabceki.Allah ya dafa mana baki daya Amin.
reply 0

Related Posts


Trending

SEARCHING🥺🥺 General
Bare Ta Auri Dan Fulani General
What is your opinion on Jigida? General
Ya yanayin Sanyi a wajen ku at this time? General
Tambaya Entertainment
TEAM LEFE DOLE KO ASOKE LEFE Marriage
Why do men do this dan Allah? General
LADIES WANT SOMEONE RELIGIOUS BUT DON'T WEAR HIJAB Relationship
Your Birthday. Entertainment
Boredom General
A Message to My Princess (unknown wife) Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure? Marriage