What's my fault if i was born illegitimate?😭😭😭
Anonymous Jun 21, 07:30 PM

What's my fault if i was born illegitimate?😭😭😭 0

Na dade ina boye damuwata amma yau zan fada dan Wallahi dakyar nake typing dinnan zuciyana kamar ze fashe😭 meyasa mutane basa yi mana adalci ni meye lefina dan an haifeni bata hanyar aure ba. Mamana tayi aure yaranta 8 she's living happily amma ni kullum cikin bakin ciki da qyama gurin mutane, gurin zama na kirki na kasa samu gurin yan uwan mamana sabida ni shegiyace ba'asan ubana ba, I'm 24years now ban samu karatun kirki ba haka na hakura yanzu almost 6times ana zuwa neman aure na ana fasawa dalilin shine bani da uba, daga mutum yaji labari seya gudu wasu kuma iyayen su su hanasu aure na😭 Ko saurayi yazo gurina haka yan uwan mamana ko yan unguwa zasuyi musu gulma na. Ya zanyi da rayuwata dan Allah ya zanyi😭😭😭 meye lefina nikam, me zanyi dan Allah na samu jin dadin rayuwa kamar kowa?😭 ya zanyi meye lefina😭😭 Yanzu nazo gurin Mamata shima zaman gidan nata ba dadi har yaranta gori sukemin ina ubanki ni yanzu bansan ma ina zanje ba😭 gaba daya duniya tayimin zafi😭 innalillahi wa inna ilaihi rajiun dan Allah kuyimin addua wallahi ji nake kamar zan mutu kamar in kashe kaina haka nake ji😭
post

Replies

(13)
Zainab bashir Jun 21, 07:56 PM
Kinada Allah shi yasan dake ki dage da sallar dare ..Allah ze kawo miki jin dadin d bakya tunani insha Allah
reply 3
Sgabdo Jun 21, 09:06 PM
subhanallah Inalillahi sorry My Sister I Feel For You
reply 0
Salma M Abdulkadir Jun 21, 09:45 PM
Kiyi hakuri, kiyita addua Ubangiji ALLAH ya baki wanda zai so tsakani da ALLAH
reply 0
Sgabdo Jun 21, 10:16 PM
Kwai jarabawa Allah Yake miki Killing your Self is failing the Test. but Make sure your situations brings you closer to Allah. pls And He will surely change your life for you
reply 1
Anonymous #1 Jun 21, 10:57 PM
Innalillahi wainnailaihi ilaihi raji'un 💔 Allah ya kawo miki yacce za kiyi 😭
reply 1
Muhammad Musa Muhammad Jun 21, 11:05 PM
Son Allah sister don't hurt yourself remember Allah yna jin komai fake faruwa dke. su Kuma 'yan uwan maman ki Allah zeyi maganin su because dabbobi ne (sorry for using the word) ki gwada sayuwar dare na 40 dyz kina fadawa Allah kukan ki am sure zki dwo ki bmu lbr Mai Dadi. remember idan kk bar gida kk shiga duniya abinda ya faru da mother nki shi zai faru dke, plz ki zauna gd Kuma ki zamanto ta kirki don nasan 'yan uwan maman ki idan zki riqa.abinda kk so ba za suyi Miki fada bh
reply 0
Funtua Jun 21, 11:27 PM
Assalam alaikum, am sorry for you 6ta, kigane kowa da Irin jarabawar da Allah yake masa, may be idan kika jajirce wannan ya zama silar Rabautarki a Lahira. Shawara ta gaba Kuma ki dage akan abinda kikasa a gaba in karatu ko aiki ko Sana'a kiyi kokari kiyi fice, ma'ana ki zama Abar kwatance a harkokin da kike wannan insha zai tura wancan Kuma kidaina nuna masu damuwarki akan haka Kuma Koda mutum ya kiraki da haka mutane zasu Mai Allah wadai.
reply 1
Anonymous #2 Jun 21, 11:28 PM
ina tare dake wlh dari nisa dari kema ai mutun ce kamar kowa kaddara ce kowa da kalar tasa karkiji komai wlh ina tare dake
reply 1
Tijjani Muhammad Jun 22, 07:24 AM
relocate to another city, where your relatives lives to start a new life. I believe if you leave the currently place you are living. zaki samu mafita and keep praying
reply 0
Abdillahi Shuaibu Jun 22, 02:49 PM
Shawara ta ki riqe Addini da kyau, kuma ki laqanci sallolin dare sosai kamar yanda wani Dan uwa yabada shawara. sannan maganar kisan kai, ki manta gaba daya. saboda kinsan matsayin Wanda ya kashe kanshi a musulunci. Dua Itace takobin Mumuni, saboda haka kar kiyi wasa da addua, in sha Allah zaki sama mafita. sannan ina baki shawara ki tsaya kiyi Karatu/Sana'a da kyau. Allah zai kawo miki mafita in sha Allah Allah yabaki ikon cin jarabawar Amin. Allah yasa mu dace Amin
reply 0
Anonymous #3 Jun 23, 05:43 AM
sorry dear can we be friends?
reply 0
Broskhalifah Jun 23, 05:57 AM
Allah sarki abun babu dad’i kam amma duk wanda kikaga yana miki hakan to yana da qarancin ilimin addini, ki cigaba da addu’a da kuma yawai sallar dare insha Allah zaki samu mafita 🙌🏾
reply 0
Anonymous #4 Jun 24, 08:11 AM
Ki cigaba da addu'a Allah zai kawo mafita, dan Allah ki manta da maganar kashe ki. In bazaki damu zanso mu zama friends.
reply 0

Related Posts


Trending

friendship Relationship
Are you ready!!! General
Dear girls, Relationship
SEARCHING🥺🥺 General
Bare Ta Auri Dan Fulani General
What is your opinion on Jigida? General
Ya yanayin Sanyi a wajen ku at this time? General
Tambaya Entertainment
TEAM LEFE DOLE KO ASOKE LEFE Marriage
Why do men do this dan Allah? General
Your Birthday. Entertainment
Boredom General
A Message to My Princess (unknown wife) Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure? Marriage