Alhaji Hamza
May 12, 11:25 AM
Matsalar saurin fushi (Anger issue)
1
Na dan jima ina ganin masu fama da matsalar saurin fushi wasu suce sun bi hanyoyi sun warke wasu Kuma su ce ba su warke ba.
Ba a batun saurin fushi ba kadai, akan komai da yake lalura ce ta cikin jiki ko ta wajenshi; magani yakan bambanta Kuma ya ta'allaka da Imanin mai lalurar.
Misali yawaita TA'AWIZI tabbas yana korar fushi, haka nan idan a tsaye ake sai a zauna..da dai sauran karashen shi ma magani ne sadidan. To amma sai mu tarar wani ya bi duk matakan amma shiru.
A gaskiya rashin imaninmu na gaske da abin shi yafi zama sanadi da ba ma ganin tasirinshi.
Haka nan ganin likitocin da abin ya shafar wanda da yawanmu a wannan zamanin mun fi yarda da ganin likitan asibiti sama da yin addu'a akan lalura (ba a hana neman magani ba) amma ni sai nake cewa; shi likitan asibiti sai yayi binkice nan-da-can, sannan ya bayarda maganin da yake da ran zai warke amma Allah da ake karanta sunayenShi da addu'a shi Yasan jikin domin shi Ya halicci jikin, kuma ciwon ikonShi ne, haka nan warakar, to na fi amince miShi.
Allah Ya hore mana lafiya Ya hore mana Imani na gaskiya, amin