Assalamu alaikum warahmatullah yan uwana musulmai, akace shirka shi ake nufi da zuwa gurin boka ko Malam ko. na dade Ina zuwa sabida matsalolin yau da kullum amma abin na matukar damuna kuma akace Allah baya yafewa😢na dena ya zaayi na kare kaina daga zuwa? Kuma Allah zai yafemun�
inason cikakken bayani nayi nadama.ina kara barar adu'a daga gareku nagode.
Alhmdullih kinyi nadama kuma kintabbatar haramunne,dama abun muni shine mutum yamutu yana yi to Alhamdulillah Allah ya ganar dake saiki dage da istigifari da adduar neman tsari.purify your heart through prayers,sadaqa da istigifari sosai kuma da nadama insha Allah komai zai daidaita.Allahu gafururrahimu ne.amma fa saikin dage kwarai da neman gafarar Allah.
Allah na yafewa. Idan mutum ya mutu bai tuba bane Allah baya yafewa.
Allah ya tsare mana imanin mu. Ya yafe mana kurakuran mu
Ai duk sharadan tuba sun cika anan; dan muna kyautata zaton Allah Ya yafe tunda haka mai Akhdari ya kawo "YIN NADAMAR ABINDA AKA AIKATA DA KUMA ALKAWARIN BAZA A SAKE KOMAWA ZUNUBIN BA" muna tayaka/ki murna, Allah Ya hore mana tuba kafin mutuwa, amin
×
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment