An tabbatar da cewa masu kutse na iya jefa manhajar tattara bayanan sirri daga nesa cikin wayoyi da sauran na'urorin shiga intanet ta hanyar yin amfani da wata babbar tawaya da aka gano a manhajar aika sakwanni ta Whatsapp.
Kamfanin WhatsApp, wanda mallakar Facebook ne, ya ce ana hakon wasu "zababbun mutane" da ke amfani da kafar sada zumunta, kuma "wani jigo cikin harkokin fasahar intanet" ne ya yi sanadin hakan.
An kaddamar da gyare-gyare tun ranar Juma'a.
A ranar Litinin kuma kamfanin WhatsApp ya bukaci dukkan masu amfani da shafinsa mutum biliyan daya da rabi su sabunta manhajojinsu don karin kandagarki.
An fara ba da rahoton wannan al'amari wanda aka gano a farkon wannan wata ne a cikin jaridar Financial Times.
Ana amfani da fasahar kira ta Whatsapp a buga wa wayar mutumin da ake hako. Kuma ko bai amsa kiran ba, manhajar tattara bayanan za ta makale wa wayarsa, kuma kamar yadda aka ba da rahoton kiran zai bace daga jerin kiraye-kirayen wayar.
WhatsApp ya fada wa BBC cewa jami'an tsaronsa ne tun farko suka gano tangardar, kuma suka yi musayar bayanai da kungiyoyin kare hakkin dan'adam da wasu kwararru kan sha'anin tsaro da kuma Ma'aikatar Shari'ah ta Amurka a farkon wannan wata.
"Harin na da duk siffofin wani kamfani da aka ba da rahoton yana aiki da gwamnatoci wajen safarar manhajojin leken asiri da ke kwace ragamar ayyukan wayoyin salula,” kamfanin Whatsapp ya bayyana ranar Litinin cikin wata sanarwa ga manema labarai.
Jaridar Financial Times ta ba da rahoton cewa kamfanin tsaron Isra'ila na NSO Group wanda a baya ake bayyana shi da "dillalin makaman da ake harbawa ta intanet" ne ya kirkiro wannan hari.
Sai dai a cikin wata sanarwa kamfanin ya ce: "Fasahar NSO an ba ta lasisi don bai wa hukumomin gwamnati iko, bisa manufar yaki da aikata lafiuka da ta'addanci".
WhatsApp ya ce ya yi wuri a san adadin masu amfani da shafinsa da wannan tawaya ta shafa, ko da yake ta kara da hare-haren da ake zargi ana kai su ne kan manyan jiga-jigai.
A cewar alkaluman baya-bayan nan na Facebook, masu amfani da shafin WhatsApp sun kai biliyan daya da miliyan 500 a fadin duniya.
Cc: bbchausa
Related Posts
Trending Discussions
Family palava
It's still on the marriage issues let me share my experience, i came home from school some months ag...
Read more
General
what's bad in delaying marriage?
kawai dan mace ta kai certain age se a matsa mata ta kawo miji ni na kasa gane abin. like what's the...
Read more
Marriage
how i feel about women
I wanted to share this to know if it is normal and some few men feel this way sometimes. i don't lik...
Read more
General
Is it okay to send nudes to your boyfriend?
my boyfriend that has promised to marry me asked me for nude pictures yesterday I don't feel comfort...
Read more
Advice
unjust love
Assalamu alaykum people,, well lemme start from the very start, well I met this guy last year, Masha...
Read more
Advice
Why ist hard for me to find true love?
Am a type of guy thats too quiet and care alot, am too emotional, i dated about 3 times, all i end...
Read more
Relationship
Friend request
Good morning
I am yet to receive a request
I hope I have’nt done any mistakes during the registr...
Read more
Advice
Warning to others! How porn destroyed my life
I write this with a heavy heart, there is a new addictive substance out there it is Porn.
It all st...
Read more
Advice
I need Advice
So I'm new here please pardon my mistakes.
I used to have intense emotions towards my partners,the...
Read more
Advice
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment