Content: |
Wasu mata biyu sun je wajen Alƙali Abu Layla don ya yi musu Shari'ah, ya ce wacece zata fara bayani.
Babbar ta ce, ƙarama ce zata fara magana.
Ƙarama: Allah ya ƙarawa Malam Imani! Wannan da kake gani Goggo na ce, na kasance ina kiranta da 'Mahaifiyata' kasancewar tun da Iyayena suka rasu ita take kula da ni har na girma. Ɗan Baffana yazo neman aurena wajenta kuma ta yadda na aure shi.
Kasancewar mijin d na aura mai kuɗi ne kuma mai tarbiyya, bayan ɗan gajeran lokaci sai ƴar Goggona ta ce, ita babu wanda take so sai Mijina kuma shi zata aura.
Goggona t rinƙa yiwa ƴarta kwalliya kala-kala tana kawota gidana, har suka fitini mijina ya afka cikin sonta. Da aka zo aure; sai Goggona ta ce, zata ba shi auren ƴarta amma bisa sharaɗi guda ɗaya tak.
Ya ce: menene?
Goggo ta ce, kasaki matarka. A take a wurin mijina ya kalle ni ya ce, ya sake ni. Ƴarta ta tare a gidan...!
Na koma muka cigaba d zama da Goggona kamar da ɗai wani abu bai faru ba. Bayan kwanaki kaɗan mijin goggona ya dawo daga tafiya...!
Nima na rinƙa fesa wanka da kwalliya, har ya afka cikin kogon soyayyata. A wannan lokacin n ce zan aure shi amma da sharaɗin sai ya saki goggona.
Ko tantama bai yi ba, ranar da aka ɗaura shi a ranar ya saki goggona, Allah ya ƙara maka lafiya kaga an yi 1 - 1 ke nan!
Alƙali ya ce: masha Allah, lalle abin mamaki baya ƙarewa. Ta ce, gyara zama Akarmakallah, ai baka ji komai ba....!
Bayan shekara guda da aurena Allah ya yiwa miijin rasuwa, shi ne Goggona tazo tana neman GADO.
Na ce mata sam bata da Gado. Muka fara hayaniya da ita, ta kirawo ƴarta da sirikinta (tsohon mijina) don su shigar mata.
Tsohon mijina ko da ya ganni, sai tuna irin alkairina da kuma yadda yaji daɗin zama dani...... Maimakon tsohon mijina ya mayar da hankali wajen zancen gadon goggona, sai ya ce, so yake n koma gidansa (Kasancewar na kammala Idda)
Na ce, na yadda zan koma yanzu-yanzu amma bisa sharaɗi... Ya ce, menene sharaɗinki? Ta ce, sai dai ka saki matarka sannan na koma. Take ya saketa b tare da ko kokonto ba.
Alƙali ya ɗora hannu a ka. Ya kalli Goggonta ya ce, menene abin da kuka kawo ƙara akai...?
Goggo: Haƙƙinmu za a bi mana Allah ya gafarta.
Alƙali: Menene haƙƙin naku?
Goggo: Akwai rashin adalci ta ɗauki Gado ita kaɗai kuma ta haɗa da mijin ƴata. Ni da Ƴata mun zama zawarawa ke nan...!
Alƙali: Wallahi baiwar Allah babu kuskure ko kaɗan cikin abin da ya faru kaɗai dai kin girbi abin da kika shuka ne ke da ƴarki.
Alƙali ya yi ta dariya abin sa. |