am i eligible for Zakkan fidda kai ?
Anonymous Mar 27, 04:26 AM

am i eligible for Zakkan fidda kai ? 0

tambaya ne dani ina aiki salary na yafi 50k shine nakesan sanin zakkan fidda kai ya halatta akaina macece ni mahaifina ya rasu
post

Replies

(2)
Abdulkarim Badamasi Mar 27, 10:15 AM
Indai kina da hali, then ya wajaba a kanki, sbd shi zakatul fitr, bashida nisab. Kuma ni ba malami ba ne, but it’s not just mandatory on you but also your dependents, (kanne, and the likes) especially if there’s no elder male in the family who’s already taking care of it. and Allah knows best.
reply 2
Mashkur wali Mar 29, 07:55 PM
*ZAKKAR FIDDA-KAI* ******************** Zakkar fidda-kai itace zakkar da ake kira Zakkar buɗa-baki, domin a banbanta ta da Zakkar dukiya. *HUKUNCIN TA:* •••••••••••••••••••• Zakkar fidda-kai, wajibi ce a kan kowane Musulmi, namiji da mace, yaro da babba, ɗa ne ko bawa. *ME AKE BAYARWA:* ••••••••••••••••••••••••• Ana bayar da kwano guda, wato muddun Nabi huɗu, a kowane mutum, daga abincin da mutanen gari sukafi amfani dashi. Idan ya zama shinkafa akafi ci a yankin unguwarku, to ita zaka ɗauka kayi da ita, kada ka bada gero, ko dawa ko masara. Amma idan mutanen unguwar sunfi cin marasa, shine mafi rinjayen abincinsu saika basu masara, kamar yadda larabawa suke bada dabino domin shine mafificin abincin su. Sannan kuma wajibi ne ka bayar da shinkafa mai kyau, kada ka bayar da abinda kai bazaka iya cinsa ba. Sannan mai gida ne yake fitarwa da iyalinsa waɗanda yake ciyarwa, bayan ya fitar wa kansa. *YAUSHE AKE FITAR DA ITA:* •••••••••••••••••••••••••••••••••••• Ana fitar da ita a rabar a safiyar sallah, kafin a tafi sallar Idi, idan kuwa aka bari har sai bayan sallar Idi, to ba zakka sunan ta ba, ta koma daidai da kowace sadaka. Amma kuma ya halatta a bayar da ita tun kwana ɗaya ko biyu kafin Idi. Domin hakan wasu Sahabban Annabi {s.a.w} suke yi. *SUWA AKE BAWA:* •••••••••••••••••••••••• Ana bayar da ita ne ga fakirai da miskinai, amma fa wannan baya nufin idan kai fakiri ne ko miskini shikenan ba zaka fitar ba. Dole ne ka bayar ga wanda yafika talauci, domin bata sauka daga kan mutum sai idan ya zama a safiyar Idi ba shida abinda zai fitar bayan ya ciyar da iyalinsa. Mutuƙar kanada abinci a gidanka, to wajibi me ka fitar, ko kuma idan ankawo maka kaima saika fitarwa kanka daga cikin abinda aka kawo maka, mutuƙar zaka sami ragowar abinci da zsi rage kuci a gida. *INA AKE KAIWA:* ••••••••••••••••••••• Idan akwai wurin da hukuma ta ware, to yana da kyau akai can, amma lallai akai a ƙalla kwana biyu kafin ranar Sallar, domin hukuma ta raba da wuri. Idan kuwa babu, to sai mutum ya rabawa fakiran da kansa. Babu laifi a bawa limami ko malamin unguwa idan fakiri ne. *KO ZA'A IYA BADA WANI ABU A MAIMAKONTA* Dole ne a bayar da abinci, sai idan babu abincin ko ba zai yi amfani ba, Kamar wasu ƙasasen da basa karɓar sadakar abinci, to saika kimanta da kuɗi ko wani abu da suke iya karɓa. *HIKIMARTA:* •••••••••••••••• Babbar hikimarta, itace ciyar da miskinai, da kuma cike kura-kuran da mai azumi yayi da ladanta. Idan mutum ya fitar da za'a cike masa inda ya sami rauni acikin Azuminsa, irinsu gulma, zagi, kallon batsa, da wasu laifuka wanda basa karya Azumi, amma suna raunana ladan Azumi, to sai a cike masa waɗannan gurare. ALLAH shine mafi sani. ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta. ALLAH ka yafe mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.
reply 2

Related Posts


Trending

Wane course ne idan mutum yayi ze samu aiki General
Buhari retire Politics
Family palava General
how i feel about women General
Addiction problem Advice
I need an advice about our relationship with my cousin Relationship
Miji na baya saduwa da ni? should i do this? Marriage
unjust love Advice
Should i do it? she's tempting me Advice
Friend request Advice
Warning to others! How porn destroyed my life Advice
What do ladies mean by "Financial stability" in men?? General
I need Advice Advice
i want to get married ???? Marriage
Looking for poetic lady Meetup
advice pls Relationship
a never ending love General