MAGANA AKAN ALJANU
Alhaji Hamza Apr 11, 04:24 PM

MAGANA AKAN ALJANU 1

Sau da yawa ina fada; mutane muna manta Allah idan wata musiba ta taso mana musamman iyaye mata. Idan an rasa miji sai ace aljanu ne, idan ana yawan ciwon kai shima aljanu ne, idan jini ya hargitse shi ma dai haka, idan za'ayi kishiya nan ma haka, kusan komai na rayuwa sai ace aljanu ne, kuma an fi yaudarar mata da wannan zancen. Waye aljani? Aljani halitta ne kamar yadda mutum yake halitta a cikin halittun Allah madaukaki, sai dai cikin iko da gwaninta ta Allah Ya halicci aljanu ne ta yadda idon mutane bazai iya ganinsu ba (a mafi yawan halaye). Amma mu sani mu mutane mun fi aljanu matsayi da kima a wurin Allah, haka nan mun fi su hatsabibanci. A ka'ida aljani ba ya sanya mutum aiki, sai dai mutum ya sanya aljani aiki, ko da kuwa mutanen da suke haduwa da lalurar shafar aljanu, suna iya samun ikon akansu. Sannan mu sani aljani matsoraci ne fiye da yadda mutum yake da tsoron aljanu, duk da kasancewar aljanu din iri-iri ne (bari mu tsaya kan batunnan haka). Yaya ake RUKYA? Yin Rukya saboda korar aljanu hanyoyi ne daban-daban, sai irin baiwar da Allah Ya baiwa mutum, shiyasa Annabin Rahma Alaihissalam Ya koyar damu addu'o'i a gabobi daban-daban, ga misali akwai aljanin kana yin addu'ar sanya tufaafi zai kone, akwai wanda kana yin ta fita gida zai kone, akwai wanda kana yin ta hawa abin hawa zai kone, akwai wanda zikiri ne yake Kona shi, akwai aljanin da ko za ka sauke Kur'ani ba abinda zai sameshi amma kuma da zarar ka juya karatun daga kasa zuwa sama zai kone (misali ka fara daga karshen Fatiha zuwa farkonta) abin ilmi Mai zurfi Kuma Mai zaman kanshi, Wanda malamai sunyi rubuce-rubuce. Amma kamar yadda nake yawan fada, ana yaudarar mata ne akan sha'anin aljanu saboda raunin Imani na mutanen yau da Allah da kuma tsananin tsoron aljani da mata suke. Ba kowani abu bane yake kasancewa aljani ne ya haddasa, ga misali; idan anzo neman aure, sai mahaifiya ko kawarta ko kawar wadda za'a aura tace wai aje wurin wani (Mai suna malami) wai ya duba yiwuwar aure, kuma wai sunan abin Istikhara! Annabi Alaihissalatu wassalaam Yana koyar da Sahabbai Istikhara kamar yadda Yake koyar dasu Kur'ani (ta yiwu muyi bayaninta nan gaba). Idan kuma an samu wani shaidani yace wai idan bai amfani daa mace ba za ta gani, sai mu tambayi kanmu; 'waye yake da iko akan komai? Idan munce Allah, to mun bi abinda Ya aiko mana AnnabinShi dashi? Tunda bamu bi ba, dole kowani dan iskan gari ya jefemu da Sihiri Kuma ya samemu (domin bamu yarda da Allah ballantana mu rika yin HIRJI irin Wanda aka koyar damu a shari'a). Mu sani, duk wanda ya/taje wurin wani wai ya duba masa/ta wani abu da zasuyi idan da alkairi ko babu, sai yayi kwana arbain (40) ya/tana sallah Allah bai karba ba (to wa ya aikemu?) To Kuma bayan haka ga laifin zina. Matsalarmu! Babbar matsalarmu a yau shine rashin neman ilmin addini daga wadanda suka san addinin da gaske ba 'yan neman kudi ko shuhura ba. Maganar da yawa idan hali yayi zan cigaba da yardar Allah. Allah Ya shiryamu Ya ganar damu, amin. Na so ace akwai ikon yin magana da murya.
post

Replies

(3)
Anonymous #1 Apr 11, 09:14 PM
Masha Allah, Allah yakara ilimi
reply 1
Alhaji Hamza Apr 11, 11:25 PM

Amin-amin Allah Ya bamu mai albarka
reply 1
Trustee Apr 13, 11:52 AM
well said
reply 1

Related Posts


Trending

Are you ready!!! General
Why is it that working class guys like me only meet idle ladies Relationship
Dear girls, Relationship
SEARCHING🥺🥺 General
Bare Ta Auri Dan Fulani General
What is your opinion on Jigida? General
Ya yanayin Sanyi a wajen ku at this time? General
Tambaya Entertainment
TEAM LEFE DOLE KO ASOKE LEFE Marriage
Guys on this app wan make me crazy Matchmaker
Boredom General
A Message to My Princess (unknown wife) Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure? Marriage