My wife became rebellious after i moved her abroad, Pls ku bani shawara
Anonymous Mar 17, 07:11 AM

My wife became rebellious after i moved her abroad, Pls ku bani shawara 2

Yau kimanin shekara takwas kenan ina wata kasa, bayan na gama karatu na a kasar na samu aiki se na cigaba da zama a kasar. Kamar shekaru 3 kenan na auri wannan yarinyar daga Kano na kawo ta wannan kasar. Komai ni nayi mata tin daga kan passport, family visa, na biya mata flight da sauransu. Da tazo nan se ta samu aiki a wani company tanayi, bayan ta fara aikin se na fara fuskantar wasu abubuwa game da ita. Akwai abubuwa da banson fada anan amma dai ina dan zargin tana wasu abubuwa da basu dace ba a gurin aikin da sauran maza abokan aikinta. Se na nemi ta dena aikin kawai ta dinga zama a gida tinda ban dauke mata komai ba, kuma Alhamdulillah ba abinda zata nema ta rasa a guri na har da wasu nata ma. Baiwar Allah nan tace ita bazata iya dena aiki ba. Kuma ni ne na samr mata aikin ma, komai ni na mata. Ta nuna itafa akan ta dena aiki sede na sake ta. Na yiwa magabatanta magana amma ina ganin kamar a baynta suke. Haihuwa yanxu kauce mata take, tinda ta haifi yaro guda daya. Bansan dalilin ta ba. Ina matukar nadamar kawota wannan kasa walh. Yanxu in na sake ta ma ba barin kasar nan zatayi ba, zanci gaba da ganinta raina yana baci. Don Allah kuban shawara ya zanyi akan wannan abu. Kuma ina kiran maza 'yan uwa da kada suyi kuskuren kawo matansu kasashen turai, don walh mata in suka goge anan fin karfin mazan su suke. Allah ya mana magani.
post

Replies

(21)
Mustapha jnr Mar 17, 07:23 AM
a gskyar mgna, u guys need to talk and understand each other .. that is the way out.
reply 0
Abdulkarim Badamasi Mar 17, 07:30 AM
I hear this is common a lot, and wlh it’s one of the reasons that made me not want to japa. Amma fa, tunda anyi hakan, first… “zargi” alone isn’t enough grounds, find proof if there is. Zama da macen da babu biyayya is hard, but ka cika da addu’a Kawai. But also, consider where you are and try to secure yourself for her not to implicate you, gather your own evidence. idan taje tayi karya cewa kayi mata duka ko makamancin hakan, kana cikin matsala… find ways to gather proof to avoid implication
reply 2
Naseeba Mar 17, 07:37 AM
abinda ya kama na farko shine ka fara tabbatar da xagin ka idan gsk ne sai kadau matakin daya dace idan kuma ba hakane ba sai ku xauna kuyi mgn ta fahimta Amman yanxu xargi kake
reply 2
Anonymous #1 Mar 17, 07:41 AM
I have some advice for you but I'm not sure of posting it here because it might be posted on Instagram and she may come across it.. You can reach me here - tincanlover@gmail.com
reply 0
Hadiiizah Mar 17, 07:53 AM
Dan Allah karka saketa in baka tabbatar ba, because you've clearly say zargin ta kake baka tabbatar ba. Shawara shine kaci gaba da Addu'a cewa inhar akwai abinda takeyi a boye wanda baka sani Allah ya bayyana maka ya kawo maka mafita mafi alkhair. Allah yasa mu dace
reply 1
Student of the year Mar 17, 08:10 AM
kawai kace mata zata zo kuzo nigeria hutu da kunzo sai ka wace passport nata kayi kokarin ayi deporting nata daga zuwa kasar kawai
reply 1
Anonymous #3 Mar 17, 09:04 AM

If you can say it here, just say it. thats why its community forum it just doesn't sit well with me, when i see such comments telling the poster to contact them privately.
reply 2
Anonymous #4 Mar 17, 09:27 AM

Abinda nayi tunani akai. He should be very romantic to her na lokaci kaden, sai yace "muzo Nigeria muyi gaisuwa". Daga ce zaiyi solving problems nasu.
reply 1
Anonymous #2 Mar 17, 10:35 AM
Assalama Alaikum Mr.I’m so sorry about this..Amman ai not all fingers are equal..ba’a rasa Nono a Ruga..Kuma kace kar mutum yayi kuskuren kawo matansu kasar turai Wallahi ba’a rasa mata na gari..Kawai Kaddarar kace samunta ahaka Kayi hakuri..Allah ya Baka wata wadda tafita Alkhairi Amin…
reply 1
Rukaiya Muhammad Mar 17, 11:49 AM
slm..dan Uwa shawarata a nan shine ka nastu ka kwantar da hankalinka and study her very well,ka ce kai kasama mata aiki kuma kai kakaita can.so if there is a way for you kasamu colleague dinta awajen aikinta ku kulla abota also be taking and bringing her home.just form some kind of gentleman to see how best you guys can go.as one of the commenter said gather your proofs enough so you can only achieve that towards been nice and gentle. also baduka mata suka zama dayaba pls.to me karka sake matsa mata akan tabar aikin for now just calm down and be strongly prayerful insha Allah komai zaixo dasauki kuma zaiwuce.
reply 0
Zainab sani kazaure Mar 17, 11:58 AM
wasu mutane sai ahankali amma gsky b duka aka taru aka zama daya ba kowa d irin halin da Mata dyw suna zaune a turai b aure ma Sun tsare mutuncin su kuma dyw suna d aure suna aiki Sun tsare mutuncin su dana iyalan su Ni Ina ganin kawai takance aka samu matsala ba a yi dace ba kuma ni Ina ganin kamar sati ba mafita bane kawai idan kun samu hutu kuxo ganin gida daga nan sai kace mata bazaka koma d ita ba k samu k San yanda zaka bullowa abin ta hanyar maslaha idan rabuwar ne ma ku rabu a gida inda kuka Saba allah y kawo maka mafita k nutsu kayi bincike k tabbatar karka biye ma zargi zuciyan ka yasa kyi abinda za kyi dana sani
reply 0
Abdulkarim Badamasi Mar 17, 02:09 PM

statistically, most people that marry here and take them there regret it. sbd, they realize they have certain level of authority and misuse it.
reply 1
Tijjani Muhammad Mar 17, 07:29 PM
bros I should advise you karkanuna Mata bachin ranka kajawota ajikin Ka show her love and caring from their sa kanuna Mata ya kamata you should come back home Nigeria for holiday. if you bring her back to Nigeria maybe you can't diverse divorce her Ka koma abinka
reply 0
Anonymous #5 Mar 17, 09:02 PM
First kasamu proofs dayawa and ba kowacce mace bane haka Allahu yazaba mana mafi alkairi amin
reply 0
Abubakar Dalhatu Sulaiman Mar 17, 09:55 PM
Gaskiya in dai ka tabbatar da zargin ka kawai ka sallameta ai rayuwa ta na da yawa in dai da hakkinka akanta kawai ka kyaleta zakaga ikon Allah
reply 0
Anonymous #6 Mar 18, 05:03 PM
come for me i promise to be obedient 🙌🙌
reply 1
Abu Jaafar Mar 19, 07:02 AM
Ka bari se Kun dawo Hutu, seize her passport and leave her in Nigeria. Kar ka sake ta.
reply 0
Anonymous #7 Mar 19, 11:26 AM
I have no advice to give but only something to say... "kana ruwa".
reply 0
KingMoha Mar 19, 01:28 PM
Gaskiya zama da macen da babu ladabi da biyayya is not easy. Your mistake is taking her there, and now the best thing is to just keep praying while trying to let her understand that you love and always remind her of Allah.
reply 0

Related Posts


Trending

Wane course ne idan mutum yayi ze samu aiki General
Family palava General
what's bad in delaying marriage? Marriage
Is it okay to send nudes to your boyfriend? Advice
Addiction problem Advice
I need an advice about our relationship with my cousin Relationship
Miji na baya saduwa da ni? should i do this? Marriage
unjust love Advice
can you marry a raped girl? Marriage
Should i do it? she's tempting me Advice
My love for him ??? should I tell him? Advice
Why it's harder for ladies to get husbands. Advice
Why ist hard for me to find true love? Relationship
Friend request Advice
I need Advice Advice
Complains General