Salamu-alaikum.
Nayi kimanin shekara 3 muna soyayya da wannan baiwar allan. Toh yanxu mahaifiyata ta nunan tana sha'awar na auri cousin dina wato 'yar kanwarta. Har sunyi magana da kanwar tata ma. Kuma gasky nima nafi son na auri cousin din nawa. 
Wannan yarinyar amma tana yawan yimin magana akan kawayenta sunyi aure, allah ya nuna mata namu da sauran maganganu dai da suke nuna tana nufin lokaci yayi nima ya kamata na yunkura ayi abin. 
Ina sonta wallahi banason nayi breaking heart dinta. So nake mu rabu cikin mutunci kar taga na yaudare ta yanda ko bayan munyi aure zamuyi zumunci. 
Tinani nake tinda wayarta ba ta yayi bace sosai na canza mata ita, farin cikin hakan ze sa ta mnta bazatace na yaudare ta ba in na gaya mata cewa zan auri wata. 
Shawara nake nema yanda zanyi
                
            
                Maganar gaskiya ka yaudare ta                
            
                kahadasu biyu kawai ka aura 
wayan nan bashi zai hana tace baka yaudareta ba                
            
                kai Malan wannan asalin yaudara kar kuma k sake wani yaudaran nata d waya kawai k fito k fada mata gsky yanda zata fahimta                
            
                Allah ya kyauta, maganar yaudara kuma na nawa , Kila ma Ka sa ta daina Kula kowa sai Kai. yanzu abi da ya rage shine fada Mata gaskiya. ita kuma Allah ya chaja Mata da Wanda y fika alkhairi ya bata hakurin jure rashinka                
            
                kutmelesi kai amma wannan guy din dan firm ne kai ko idan ba haka ba a shekara ukun karatu kake koya mata, ku dinga jin tsoran Allah wallahi ku dinga tuna kuma kuna da yan uwa mata shekara uku kana tare da ita da sunan soyayya yanzu da take ganin lokaci yazo karshe kuma ka dinga mgn zaka siya mata waya ka rabu da ita. ALLAH ya sawake kayi hakan kawai tunda tun yanzu hakan ya fara zuwa tunaninka ita kuma Allah ya bata wanda ya fika alkairi                
            
                Wallahi this will break her heart more💔not you will leave her for anything else amma wai zaka rabu da itaa saboda wata? Kaiiii Ikon Allah, gaskiya inkayi haka akwai matsala... And you are talking ka sawo mata waya this will not make her heart not to break💔and if you talk to your mom kace mata akwai wanda kuna tare 3years now and you don’t want to break her heart to zata fahimce ka idan uwa tagari ce, sorry☹️ Allah ya rabamu da maza mai irin wannan halin ya Rabb🙏🤲and kaima Allah yasa ka gane🤲                
            
                Mahaifita amma kamar gaba take da ita ko? Allah yasan ba nufina kenan ba akanta                
            
                Ai ba'a haka. Da hakan me yiwuwa ne da bakan zanyi don duk ina sonsu                
            
                Dama dole ai zan fada mata, amma wayar nake gani kamar zatai compensating na jirana da tayi.                
            
                Ni ban hanata kula kowa. Tanada wani ko batadashi ni ban sani ba                
            
                Komai Allah ke tsara shi. Allah yasan banida nufin cin zalinta ko kuntata mata                
            
                Ni kam mahaifiyata ma ta nemi raayina ne, amma ni kam sha'awarta dana gani da abin nakeson na faranta mata. Tana yawan yimin maganar cousin din nawa. 
Farin cikin mahaifiyta kamar yafi na wannan yarinyar ai ko?                
            
                Allah dai yasan Mai gaskiya kuma yasan manufar mu Akan Yan uwanmu .mu yanzu baza mu iya yanke hukunci ba tukun.Amma dai abin da ya fi Ka fada Mata gaskiya domin ta fara sabawa da rashin Ka tun yanzu                
            
                Yes farincikin mahaifiya shi mukeso amma be careful with this decision, you will make your mom happy and break a girl's heart.... anyway Allah ya zaba maka mafi Alkheri and ita ma Allah ya zaba mata mafi Alkheri😊🤲
Muma Allah ya zaba mana mafi Alkheri🤲                
            
                to gsky de k ajiye zancen waya Agefe kuma k daina wani fada mata magana me dadi a waya kaje gida ku zauna da ita k mata bayani yadda zata fahimta k bata hkr sosai kila allah yayi ba matar ba bace amma dole ka karya mata zuciya alaji                
            
                why why why some men are like this 😑😑😑😑 this is horrible maganan gaskiya Ka yaudare ta kuma Allah zai sakamata                
            
                Oga mgnr gaskiya ka dai na sonta ne may be kai baka gama fahimtar hakan ba tunda dai Allah yasa baa sa rana ko anyi aure ba tun yanzu kawai ka fadamata ta nemi wani ko dan bata mata lokacinnan da kayi ALLAH ba zai barta haka ba zai bata wanda ya fika alkairi inshaallah                
            
                wai inasonta, tunda kace cousin dinka kakeso bakasonta fakat.....angulu da kan zabo                
            
                karyane dama ba sonta kake ba zancen yaudara ka riga ka yaudareta ka bata mata lokaci sai dai ka jira sakayya tsakaninku                
            
                seems like you've already made up your mind. hope it's for the best.                
            
                Malam Yaudara kam kana shirin yi, kasan kana so ka auri cosine naka then why keeping her around for 3years. Irin kune kuke bata mana suna wallahy                
            
                Dan Ma rainin Hankali wai kana so ku cigaba da mutunci even after your marriage, wallahi wallahi Allah ba zai barka ba I'm telling you this as a Guy ba ba luck nake yi ma adua ba but that's the blunt truth                
            
                Kuma Allah yasa dai baka lalatata ba, though it takes to tangle                
            
                This is not reasonable at all
 u want to compensate her with a phone because she have no emotions koh. This is pure yaudara wlh                
            
                Dan uwa maganar gaskiya qila daman bada aure kakesontaba shiyasa saboda inhar dagaskene kunyi tsawon shekarunnan daka fada bey kamata arana tsaka kace wani abuba.natabbata inhar mum dinka tasanta kuma tasan kanada niyar aurenta bazata tirsasamaka akan dole saika aure cousin dintakaba.pls dont buy her anything at the end run kayi punishing dinta by you bad news ba.call her sat her down and tell her ur so called excuse of not marrying her aftral macce bata auren mijin daba nataba.Allah yasa mudace.                
            
        ×
        
    
    
 
                         
                    
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment