Anonymous
Feb 7, 09:45 PM
Taimakon juna
1
Tun kwanakin baya nakeso nayi magana/na tattauna akan wani abu da ya faru da ni.
Dan lokutan da suka gabata na shiga wani juyi na rayuwa wanda da yawa a wurin irinmu (normal) ne, irin mutum kawai ya shiga rashin kudi, sana'o'i da harkoki su tsaya, ga shi kuma zuwa neman taimako da nauyi/kunya musamman sanin irin dabi'armu ta mutanen yau. Azumin bara mun jera 15-20 days muna sahur da shan ruwa da kunu alone and sometimes ma babu, and this is someone da yake da businesses wurin 3-4 duk they were running fine till lately.
To abinda yasa nayi wannan rubutun shine; muna tsakiyar wannan tsananin; sai aka min sata a gidana, sai abu ya kara taazzara, I decided to contact a friend (so-called) nace ga matsalar amma aron wani adadi na kudi nakeso kadan, na fara sabon jari tunda Alhamdulillah na iya abubuwa da yawa, after listening to me, sai ya kawo excuses dinshi, amma we have alumni group na makaranta, he'll talk to them, I hesitate at first but given the situation I later gave in. Yayi mgn, and the president of the association called and asked details (I reassured him cewar aro nakeso ba kyauta ba).
Daga ranar sai duk su biyun suka daina amsa wayata ko replying WhatsApp message dina (mark you, wayar da nake rikewa ko N5k baza a saya ba. Saboda a wancan lokacin someone told me to sell my phone) and maganar (data) I am using a free-data app (Stark VPN).
To bayan wasu 'yan kwanaki sai a cikin wannan group dinnamu na Alumni, aka nemi a tara wani kudi domin wani PARTY/CELEBRATION; ga mamakina sai ga shi a cikin kasa da wata daya (1 month) anyi raising more than N300k, while ni kuma abinda na nemi aro shine N100k or less.
Manufar rubutun shine jan hankalinmu duka, mu koyi fifita maslahar juna fiye da son kanku. What I feel is, yin PARTY ya fifici fitar da dayanmu daga cikin matsalar da kowa na iya tsintar kanShi a ciki.
Na takaita rubutun don gudun matsawa mai karatu dan haka it isn't detailed.
Allah Ya sa mu gyara, amin