Alhaji Hamza posts

Posts History

    Title: My opinion on INTEREST (KUDIN RUWA)
    Content: Dukkan Dan Adam Mai sabo ne mafi alkairin masu sabo shine mia tuba. Na ga an tattauna akan cin bashi daga wasu manhajoji, sai nayi mamaki yadda abin ya zama kamar babu komai, sai kawai mu cewa kanmu lalura ce kuma muyiwa kanmu izinin cin kudin ruwa. Kudin ruwannan shine Allah Ya ce Mai cin shi ya shirya yaki daShi a kiyama. Ya kamata muyi kokarin lura da kyau mu kuma Kara sanin addininmu, Dan wannan ba abin wasa bane, ko da mai unguwarku aka ce za kuyi yaki ai ba abin wasaa bane ballantana da Rabbil Izzati kuma a taron kiyama. Kuma mu sani kudin riba rushe dukiya yake komai daren-dadewa. Allah Ya warware mana Ya hore juriya da karfin Imani.
    Category: General Jul 21, 11:43 AM
    Title: Regarding forming a productive circle for like minds in business
    Content: Yawwa munyi magana Mai Dan tsawon kan topic dinnan, har munyi suggesting samar daa group, so we have one now tare da daga 'yan wannan platform din, though bamuji ba daaga admin team na gidan, but check the post we had back. Nagode
    Category: General Jun 22, 05:56 PM
    Title: Na kasa fahimtarmu
    Content: Kullum za ka ji wancan/waccan suna fama da matsalar (istimana'i/masturbation) wasu kuma neman mata, wasu bin maza, wasu bin jinsunsu (Allah Ya kiyayemu duka). Amma kuma kullum kara yakar aure muke daa karfinmu, daga zancen sai ta gama karatu, saai zancen sai ya samu aiki. Yana da kyau a samu aiki da sauransu, amma tsakaninmu daa Allah akwai wanda yana samun kudade ko ta hanyar aiki ko daga iyaye wanda sun isheshi ya rike mata biyu ma (I have proofs). Amma abin talauci mu muke karawa auren tsada kuma mu rika korafi, haka nan wadanda ba tunaninmu/addininmu daya ba daga wasu kasashen wai suna fada mana muna aure da wuri kuma mun hau mun zauna, ni na yarda indai muka tafi a haka to yanzu matsalolinmu suka soma. Mu koma turbar Allah da Ma'aiki Alaihissalatu wassalaam mu ga abin mamaki. Matasa (maza da mata) muyi aure, sanadin arziki mai karfin gaske (idan anyi shi yadda shari'a ta tanada) mai tsoron talauci shi yake dauwama a talauci. Shi Allah mawadaci ne wadata mara misali. Bissalam
    Category: General Jun 18, 02:54 PM
    Title: Forming a Productive Cycle
    Content: Su waye business minded people; me zai han ayi wani cycle na like minds (and honest personalities) sbd a rika karar da juna on growth and dev., yawanci more heads a beta than one. May be if someone read my mind well can shed more light
    Category: General Jun 8, 05:29 PM
    Title: Matsalar saurin fushi (Anger issue)
    Content: Na dan jima ina ganin masu fama da matsalar saurin fushi wasu suce sun bi hanyoyi sun warke wasu Kuma su ce ba su warke ba. Ba a batun saurin fushi ba kadai, akan komai da yake lalura ce ta cikin jiki ko ta wajenshi; magani yakan bambanta Kuma ya ta'allaka da Imanin mai lalurar. Misali yawaita TA'AWIZI tabbas yana korar fushi, haka nan idan a tsaye ake sai a zauna..da dai sauran karashen shi ma magani ne sadidan. To amma sai mu tarar wani ya bi duk matakan amma shiru. A gaskiya rashin imaninmu na gaske da abin shi yafi zama sanadi da ba ma ganin tasirinshi. Haka nan ganin likitocin da abin ya shafar wanda da yawanmu a wannan zamanin mun fi yarda da ganin likitan asibiti sama da yin addu'a akan lalura (ba a hana neman magani ba) amma ni sai nake cewa; shi likitan asibiti sai yayi binkice nan-da-can, sannan ya bayarda maganin da yake da ran zai warke amma Allah da ake karanta sunayenShi da addu'a shi Yasan jikin domin shi Ya halicci jikin, kuma ciwon ikonShi ne, haka nan warakar, to na fi amince miShi. Allah Ya hore mana lafiya Ya hore mana Imani na gaskiya, amin
    Category: General May 12, 11:25 AM
    Title: Meyasa wasu masu kudi suka fi investing a transport da real estate?
    Content: Wai me yasa yawanci masu kudi a hannu sun fi mayarda hankali akan siyan baburan napep, gina plaza da gidajen haya a matsayin hanyar juya kudi? Alhalin ga sana'o'i nan barkatai masu riba tsububu ba iyaka?
    Category: Business May 7, 08:03 AM
    Title: MUNA FA CIKIN MUSIBA 1
    Content: Bismillah, wato ni a fahimtata kamar bamu gane a cikin irin musibun da muke ba, amma mun tsakar musiba ta addini da zamani tsamo-tsamo ya kamata mu farka mu kuma Hankalta. Babban magani shine mu Kai kanmu mkaarantun neman ilmin addini na malaman da suka san addinin da gaske, sannan mu Kai 'ya'ya da dangi, mu kuma koyar da iyali. Domin muna cikin zamanin da mutum zai wayi gari da Imani kafin yammaci ya koma kafirci (Allah Ya kiyayemu). Ga shi bamusan ciwon kanmu ba, bamu San su waye mu ba, mun kasa gane daga ina muke, a ina muke, kuma ina za mu je. Allah Yasa mu farka kafin muyi 'FARGAR JAJI' Amin . Sai a rubutu na gaba Insha Allah
    Category: General Apr 15, 12:02 AM
    Title: ZABEN ABOKIN ZAMA
    Content: Ni dai nakan ce, matsalar da aketa magana akan zaben abokin zaman aure; muna bari jaki me, mu rika bugun taiki. Dalilina shine, iyaye a yanzu sun cire/ an cire hannunsu daga zabarwa yaransu (maza da mata) abokin zama, sai dai idan yaran sun gama sharholiyarsu sannan a nemi iyaye su daura aure sau da yawa. A ka'ida iyaye ne za su duba Wanda ya cancanta ga 'yarsu/dansu sai su zaba musu, domin wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi, ballantana Wanda shi ya haifeka, to sai aka ce mana wannan sunanshi auren dole, kuma duk muka yarda (Dan haka iyaye suka janye hannunsu, mu kuma 'ya'yan muke gaban kanmu). Sannan mun daina neman zabin Allah sai a Baki kawai, za'ayi aure an tafi wurin boka ko dan duba, ko kuma idan anyi Istikhara ta shari'a to amma akwai abinda mutum ya zabarwa kanshi already kawai yayi ta ne a matsayin zaiyiwa Allah wayo. Ko kaji muna 'ai baza mu iya hakurin da kakanninmu sukayi ba a zaman aure saboda mun waye' to tunda bazamu iya abinda sukayi ba; ai bazamu sa rai da samun sakamako irinnasu ba kuwa (ko a makaranta idan bazaka iya nacin da wancan yakeyi ba da juriya wajen karatu ai kasan sakamkonku bazai zama dai-dai ba. Allah Ya sa mu farka da wuri.
    Category: Marriage Apr 12, 05:27 AM
    Title: MAGANA AKAN ALJANU
    Content: Sau da yawa ina fada; mutane muna manta Allah idan wata musiba ta taso mana musamman iyaye mata. Idan an rasa miji sai ace aljanu ne, idan ana yawan ciwon kai shima aljanu ne, idan jini ya hargitse shi ma dai haka, idan za'ayi kishiya nan ma haka, kusan komai na rayuwa sai ace aljanu ne, kuma an fi yaudarar mata da wannan zancen. Waye aljani? Aljani halitta ne kamar yadda mutum yake halitta a cikin halittun Allah madaukaki, sai dai cikin iko da gwaninta ta Allah Ya halicci aljanu ne ta yadda idon mutane bazai iya ganinsu ba (a mafi yawan halaye). Amma mu sani mu mutane mun fi aljanu matsayi da kima a wurin Allah, haka nan mun fi su hatsabibanci. A ka'ida aljani ba ya sanya mutum aiki, sai dai mutum ya sanya aljani aiki, ko da kuwa mutanen da suke haduwa da lalurar shafar aljanu, suna iya samun ikon akansu. Sannan mu sani aljani matsoraci ne fiye da yadda mutum yake da tsoron aljanu, duk da kasancewar aljanu din iri-iri ne (bari mu tsaya kan batunnan haka). Yaya ake RUKYA? Yin Rukya saboda korar aljanu hanyoyi ne daban-daban, sai irin baiwar da Allah Ya baiwa mutum, shiyasa Annabin Rahma Alaihissalam Ya koyar damu addu'o'i a gabobi daban-daban, ga misali akwai aljanin kana yin addu'ar sanya tufaafi zai kone, akwai wanda kana yin ta fita gida zai kone, akwai wanda kana yin ta hawa abin hawa zai kone, akwai wanda zikiri ne yake Kona shi, akwai aljanin da ko za ka sauke Kur'ani ba abinda zai sameshi amma kuma da zarar ka juya karatun daga kasa zuwa sama zai kone (misali ka fara daga karshen Fatiha zuwa farkonta) abin ilmi Mai zurfi Kuma Mai zaman kanshi, Wanda malamai sunyi rubuce-rubuce. Amma kamar yadda nake yawan fada, ana yaudarar mata ne akan sha'anin aljanu saboda raunin Imani na mutanen yau da Allah da kuma tsananin tsoron aljani da mata suke. Ba kowani abu bane yake kasancewa aljani ne ya haddasa, ga misali; idan anzo neman aure, sai mahaifiya ko kawarta ko kawar wadda za'a aura tace wai aje wurin wani (Mai suna malami) wai ya duba yiwuwar aure, kuma wai sunan abin Istikhara! Annabi Alaihissalatu wassalaam Yana koyar da Sahabbai Istikhara kamar yadda Yake koyar dasu Kur'ani (ta yiwu muyi bayaninta nan gaba). Idan kuma an samu wani shaidani yace wai idan bai amfani daa mace ba za ta gani, sai mu tambayi kanmu; 'waye yake da iko akan komai? Idan munce Allah, to mun bi abinda Ya aiko mana AnnabinShi dashi? Tunda bamu bi ba, dole kowani dan iskan gari ya jefemu da Sihiri Kuma ya samemu (domin bamu yarda da Allah ballantana mu rika yin HIRJI irin Wanda aka koyar damu a shari'a). Mu sani, duk wanda ya/taje wurin wani wai ya duba masa/ta wani abu da zasuyi idan da alkairi ko babu, sai yayi kwana arbain (40) ya/tana sallah Allah bai karba ba (to wa ya aikemu?) To Kuma bayan haka ga laifin zina. Matsalarmu! Babbar matsalarmu a yau shine rashin neman ilmin addini daga wadanda suka san addinin da gaske ba 'yan neman kudi ko shuhura ba. Maganar da yawa idan hali yayi zan cigaba da yardar Allah. Allah Ya shiryamu Ya ganar damu, amin. Na so ace akwai ikon yin magana da murya.
    Category: General Apr 11, 04:24 PM