Mai Nama Kano posts

Posts History

    Title: Jiya daddare aka sace Generator din Masallacin mu, cikin ramadan fa
    Content: Muna kokarin samun shimfidar masallaci sai ga shi an sace Generator masallacin jiya da dare. Haba mana a cikin Ramadana fa, Allah Ya shiryamu
    Category: General Mar 24, 08:32 AM
    Title: Talauchi a rayuwa ga wanda a da yake da wadata
    Content: There's this friend that I know, before he got married yana da wadata sosai Dan a lokacin dayan shagonshi nake Kai printing, to amma kowa da irin jarrabawar rayuwa da yake haduwa da ita, bayan aurenshi komai ya rika rushewa kamar movie, yanzu Babu shagon ko daya, azumin last year they hardly get kunu suyi sahur da buda-baki, haka yanzun ga wannan azumin ya zagayowa wallahi dai sammakal. Wancan lokacin I personally helped yadda zan iya, so also now. Abin da ya Kara ban tsoro da duniya kenan, idan fa yau kaine to gobe waninka, mutumin kirki kwarai ga son taimako, amma yanzu da yawan wadanda ya taimaka sun guje masa, ga wannan azumin an fara, shi ma dai hakan yake, jiya yake fada min he almost cried, " wai ace mutum ya gagari samun jari ko na 50k ma for a start a garin Kano", I just kept 🤐. Abin takaici wai 'yan uwanshi zaginshi suke suna matarshi ce take hana shi taimaka musu tunda yayii aure sun kasa fahimtar halin da yake ciki. In fact gidan haya yake yanzu. Dan dai kawai he's strong ne wallahi, and I think sbd alakarshi da wani babban malami (Faqihi) ne anan Kano yasa yake iya juriya haka. Pls idan muna da 'yan uwa Kuma muna da iko let's be helping them (he was telling me jiya he trekked for 2 and half hours to home sbd Babu and he came out to hustle today). Allah dai Ya kara rufa mana asiri
    Category: General Mar 23, 02:04 PM
    Title: why do people look down on you for not having abin duniya? (my experience)
    Content: A wuraren shekarar 2019/20 na koyar da Photography da Graphic Design in an online class on WhatsApp and later in the NH classes on Telegram. A cikin wadannan classes dinne na hadu da wata baiwar Allah anan Kano, tana sayar da irin kayan motsa Baki. Tunda dalibata ce sai naga bari nayi patronizing dinta, rannan nayi order din Shawarma, sai nace zanje na karba tunda a lokacin wurin da nake aiki ba nisa da gidansu, da Magriba naje, na kirawo waya cewar na karaso. Sai na nemi dan wani loko na make, da fito sai ta kirawo wayata, ina amsawa sai cewa tayi "A wani mota kake ne?" da murmushinta a fuska😊 ni ko nace: "Ai a sayyada ta nake" kawai baiwar Allah sai ta canza fuska ta juya, ta baiwa kaninta sakon, kafin na karasa kuma sai naga ta dawo amma dai babu walwala kamar farko😂. Kuma dai gidansu ba na talakwwa bane bare ace. Bayan wannan ma naje hoton wani biki, mun sauka a Napep angon sai cewa yayi au wai dama baka da mota?😒 Na dai hadu da irin tambayar sau da yawa kuma gaskiya banjin dadinta, yawanci mutane ko da basu da mota/abin duniya idan kai ba ka dashi sai su rika degrading dinka. Allah Ya arzurta daga taskarShi Ya hore mana ziyarar Annabi Alaihissalatu wassalaam
    Category: Lifestyle Feb 23, 10:46 PM
    Title: Team Kdramas
    Content: Ina masoyan Kdramas let's team up, a bamu movies🤗
    Category: Entertainment Feb 20, 09:31 AM
    Title: Barar Addu'a
    Content: Assalamu alaikum, dan Allah wanda duk ya ga wannan, to ina rokon addu'ar; Allah Ya sa ina da rabon ziyarar Annabi Alaihissalatu wassalaam anan kusa da duk mai burin hakan ma. Amin Allah Ya amsa mana Jarmai
    Category: General Feb 17, 05:58 PM
    Title: Ziyarar Annabi Alaihissalatu wasslaam
    Content: Ni tun tsawon lokaci nake ta buri da kwadayin zuwa Madina, nasan duk musulmi na da wannan burin, amma kowa da iyakar na shi, sai dai rashin iko yana shinge ni. Kullum ina burin gamuwa da sanadin tafiyata ko a mutane ko a wasunsu. Allah Ya mana alfarmar ziyarar da maimaici, Amin.
    Category: General Feb 15, 07:51 PM
    Title: Friendship
    Content: A wasu rubuce-rubuce na ga wata tayi magana akan samun friends and staying long with them, kuma ni ma I find it hard to make friends and stay long, sai dai hello-hi kawai, ashe I am not alone on the table.
    Category: Lifestyle Feb 11, 09:35 PM
    Title: ZIKIRAN DA AKEYI NA SHARE FAGEN RAMADAN
    Content: RAJAB 1-10th ISTIGFARI 3000 kullum 11-30th ISTIGFARI 2000 kullum SHA'BANA 1-10th HAILALA 3000 kullum 11-30th HAILALA 2000 kullum RAMADAN 1-10th SALATI 2000 kullum 11-30th SALATI 3000 kullum Allah Ya sa mu dace
    Category: Religion Feb 10, 07:49 AM
    Title: Domin samun albarka a gidajenmu
    Content: Ana karanta karshen Suratul Fathi: "Muhammadurrasulullah....." zuwa karshe kullum safe da yamma sau 1/3/. Sannan a koyawa yara domin albarka na sauka a gidan da ake karantawa. Allah Ya mana albarka
    Category: Religion Feb 9, 07:18 PM
    Title: Ance wannan hadin yana Maganin Diabetes
    Content: A samu GORUBA DA ZOGALE a dafa su kamar shayi sai a rika sha safe da dare, sannan ko yaushe aka sha sai a ci CUCUMBER guda daya. Har tsawon makonni biyu
    Category: Health Jan 27, 09:11 PM