Broskhalifah posts

Posts History

    Title: Meyasa mutane muke haka ne ??
    Content: Assalamu Alaekum Wai meyasa mutane bama gudun 'batawa 'yanuwanmu rai ne ?? regarding wacce tace an haifeta ba da aure ba meye laifinta don Allah ?? Qaddarace fah Allah ya d'aura akanta ko da kuwa iyayenta sun aikata hakan don son zuciyarsu ne, kuma duk duniyar nan babu wanda zaiso ace bashi da uba, sannan wannan abu baifi qarfin Allah ya qaddarashi a kaina ko akanka ba amma Allah baiyi hakan ba saika gode mai bawai idan Allah ya qadarta ya fad'a kan waninka kazo kana ci mai mutunci akan hakan ba. Don Allah musan mezamu dinga fad'awa 'yanuwanmu kuma karmu manta da hadisin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da yake cewa duk wanda ya yarda da Allah da kuma ranar qarke to ya fad'i alkhairi ko kuma yayi shiru.
    Category: General Jun 23, 06:08 AM