Leken asiri ta Whatsapp
Anonymous May 16, 02:00 PM

Leken asiri ta Whatsapp 3

An tabbatar da cewa masu kutse na iya jefa manhajar tattara bayanan sirri daga nesa cikin wayoyi da sauran na'urorin shiga intanet ta hanyar yin amfani da wata babbar tawaya da aka gano a manhajar aika sakwanni ta Whatsapp. Kamfanin WhatsApp, wanda mallakar Facebook ne, ya ce ana hakon wasu "zababbun mutane" da ke amfani da kafar sada zumunta, kuma "wani jigo cikin harkokin fasahar intanet" ne ya yi sanadin hakan. An kaddamar da gyare-gyare tun ranar Juma'a. A ranar Litinin kuma kamfanin WhatsApp ya bukaci dukkan masu amfani da shafinsa mutum biliyan daya da rabi su sabunta manhajojinsu don karin kandagarki. An fara ba da rahoton wannan al'amari wanda aka gano a farkon wannan wata ne a cikin jaridar Financial Times. Ana amfani da fasahar kira ta Whatsapp a buga wa wayar mutumin da ake hako. Kuma ko bai amsa kiran ba, manhajar tattara bayanan za ta makale wa wayarsa, kuma kamar yadda aka ba da rahoton kiran zai bace daga jerin kiraye-kirayen wayar. WhatsApp ya fada wa BBC cewa jami'an tsaronsa ne tun farko suka gano tangardar, kuma suka yi musayar bayanai da kungiyoyin kare hakkin dan'adam da wasu kwararru kan sha'anin tsaro da kuma Ma'aikatar Shari'ah ta Amurka a farkon wannan wata. "Harin na da duk siffofin wani kamfani da aka ba da rahoton yana aiki da gwamnatoci wajen safarar manhajojin leken asiri da ke kwace ragamar ayyukan wayoyin salula,” kamfanin Whatsapp ya bayyana ranar Litinin cikin wata sanarwa ga manema labarai. Jaridar Financial Times ta ba da rahoton cewa kamfanin tsaron Isra'ila na NSO Group wanda a baya ake bayyana shi da "dillalin makaman da ake harbawa ta intanet" ne ya kirkiro wannan hari. Sai dai a cikin wata sanarwa kamfanin ya ce: "Fasahar NSO an ba ta lasisi don bai wa hukumomin gwamnati iko, bisa manufar yaki da aikata lafiuka da ta'addanci". WhatsApp ya ce ya yi wuri a san adadin masu amfani da shafinsa da wannan tawaya ta shafa, ko da yake ta kara da hare-haren da ake zargi ana kai su ne kan manyan jiga-jigai. A cewar alkaluman baya-bayan nan na Facebook, masu amfani da shafin WhatsApp sun kai biliyan daya da miliyan 500 a fadin duniya. Cc: bbchausa
post

Replies

(1)
iamHamid May 16, 03:56 PM
toh ana nufin hackers wai. Allah ya kiyaye mu daga sharrin su
reply 1


Related Topics


Trending